Bello Turji, kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman Jihar Zamfara da kewaye, ya tsere daga maboyarsa sakamakon luguden wuta da dakarun sojin sama ke yi babu kakkautawa.
Majiyoyin Aminiya sun shaida mata cewa dakarun sojin sun lalata maboyar ’yan bindiga da dama a wasu hare-hare da jiragen yaki suka kai musu.
- An janye dakatarwar da aka yi wa Shugaban Majalisar Dokokin Filato
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 950 a Najeriya —DHQ
Sun bayyana cewa, luguden wutar ya sa karfi da yaji Turji da yaransa ficewa daga maboyarsu da ke dajin Shinkafi.
Majiyoyin sun ce Turji da yaransa sun kafa wani sabon sansani a Dajin Gando da ke Karamar Hukumar Bukkuyum a jihar.
Gando kauye ne da ke da nisan kilomita 35 daga garin Bukkuyum, Hedikwatar karamar hukumar.
’Yan bindiga dai na cin karensu babu babbaka a yankin da sauran kauyukan da ke makwabtaka da su.
Mazauna yankunan sun ce sojoji sun tarwatsa maboyar ’yan bindiga, inda yawancinsu suka tsere a kan babura, wasu kuma a kan shanu.
“Shugaban ’yan bindiga Shehu Bayade ya kware wajen satar mutane da dabbobi a yankunan Anka, Bukkuyum da Karamar Hukumar Gummi a jihar nan.
“Muna kyautata zaton Shehu Bayade ne ya gyyato Turji da yaransa don ba su mafaka daga ruwan wutar da sojojin saman ke musu.
“Muna cikin tashin hankali. Muna rokon dakarun soji da su tsaurara matakan yakar ’yan bindiga zuwa yankin nan, idan ba haka ba kuwa za su iya kwace ikon yankin gaba daya,” a cewar wata majiya.
Mun yi kokarin samun karin bayani daga Kakakin ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma ba mu same shi ba, har muka kammala hada wannam rahoto.
Turji dai ya kware wajen yi wa mutane kisan gilla da kuma garkuda mutane domin karbar kudin fansa a yankunan Shinkafi, Sabon Birni da Isa na jihohin Zamfara da Sakkwato.
A baya-bayan nan ya sako sama da mutum 50 da ya yi garkuwa da su, ciki har da mata masu juna biyu.
Ana ganin sakin mutanen da Turji ya yi, wata dabara ce ta neman yin sulhu da gwamnati.
Sai dai kuma wasu ’yan bindiga da ke kaura daga yankin da sojojin ke ragargaza sun kashe sama da mutum 60 a wasu kauyuka, kwanaki kadan bayan sako wadancan mutanen da Turjin ya yi.