✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Lokacin mulkinsa ba mu yawo da masu tsaronmu – Bala Shagari

Aminiya ta zanta da babban dan marigayi Alhaji Shehu Shagari, Kyaftin Muhammad Bala Shagari Sarkin Mafaran Shagari, mai shekara 69. Ya bayyana rasuwar mahaifinsa da…

Aminiya ta zanta da babban dan marigayi Alhaji Shehu Shagari, Kyaftin Muhammad Bala Shagari Sarkin Mafaran Shagari, mai shekara 69. Ya bayyana rasuwar mahaifinsa da abin bakin ciki a wurinsa, domin marigayin ya wuce uba a gare shi, malami  ne da yake kwaikwayo.

 

Me za ka ce kan halayyar mahaifinka marigayi Shehu Shagari  game da ku iyalinsa?

Halayyar marigayi da ya yi da mu abar so ce da kauna domin shi ba mutum ne mai tsaurarawa ba. Yakan bai wa mutum dama ya zabi abin da yake so amma da shawara, in kuma ka ki daukar shawararsa ba zai hana ka yin abin da kake so ba, matukar bai saba wa shari’ar Musulunci ba. Hakan ya sanya dukanmu ’ya’yansa muke dogaro da kanmu ba tare da la’akari da matsayinsa a kasar nan ba. Ta’aziyar da ake yi ko’ina a kasar nan ta nuna yadda mahaifinmu ya yi rayuwarsa da sauki.

Wadanne abubuwa za ku rika marigayin da su?

Abubuwan da za su sa mu rika tunawa da shi ba zan ce maka ga daya ba, domin suna da yawa amma dai ka sani bai koya wa ’ya’yansa girman kai da jiji-da-kai, wai su ji su ’ya’yan wani ne a kasar nan ba. Shi ne ya sanya muka zauna da mutane lafiya. Lokacin da yake mulki na sha tuka mota daga nan Sakkwato zuwa Legas, ba wani dan rakiya, babu wani dan gidanmu da ke yawo da wadansu matsara lafiyarsa, amma a zamanin yanzu ’ya’yan Shugaban Kasa in za su fita da ’yan rakiya suke fita. A lokacin da aka yi masa juyin mulki wani abokina ya same ni zan hau doki yake ba ni labarin cewa an yi juyin mulki. Na ce masa to me zan yi? Na ci gaba da sabgata. Ya tambaye ni wai ko ban yarda ba ne? Yana mamaki, ni ko a jikina, don tarbiyyar da ya ba mu ba ta barin mu dauki wani yana iya yin abin da Allah bai yi ba. Rayuwar marigayi abar sha’awa ce da kowa ke son yin irinta. Mun dauki koyarwarsa ta daya muke da kowa ba wani bambanci. Za ka ga abokanmu har wadanda ba su yi karatu ba, abokaina da muka taso tare da su cikinsu akwai makanikai da direbobi, haka muke zamanmu tare da su lafiya.

A Sakkwato kowa ya san kudirin marigayi na farfado da ilmi a jihar, za ku dora daga inda ya ajiye?

Za mu yi gwargwadon hali abin da muke iyawa, don ba mu iya cike gurbinsa. Rayuwar Turaki daban ce, shi ne ya dora tubalin ginin Abuja amma har ya sauka ba ya da ko fili a cikinta. Bayan an sake shi ne fa wani Babban Sakatare dan Nasarawa ya nemi ya zagaya da Turaki don ya ga ci gaban da aka samu a tubalin da ya dora. Bayan sun kammala ne yake tambayar Turaki ina gidansa? Yake fada masa ba ya da gida a nan nan fa. Ya ce ba za a yi haka ba. Ya bayar da fom a cika, ni na cika fom din na mayar. Koda na zo an dauke Babban Sakataren daga wurin. Na kai fom din wajen Minista Gado Nasko, shi ne ya ba shi fili a Abuja. An shekara 10 ba a gina komai a filin ba don ba ya da kudi. Obasanjo ne da ya zo ya gina masa gida a filin da aka ba shi. Shi kadai ne gidansa a Abuja. Dukanmu ’ya’yansa ba mu da gida a Abuja. In ka cire wadanda ke siyasa cikinmu.

Ku nawa ne ya haifa ’ya’yansa?

Ni ne babba a cikin maza, ina da yaya mace da ke gabana. A yanzu shekaruna 69, in watan Maris na wannan shekara zan cika 70. Mu 18 ne ya haifa maza 10, mata 8. Ya bar matan aure biyu da jikoki da dama.

Ko akwai wata wasiyya da bar muku?

Mahaifimu bai taba rikon kowa a ransa ba, ya ce bai rike da kowa; duk wanda ya yi masa wani abu ya yafe wa kowa, bai kwana da fushin kowa ba. A Kuduna ma wajen kaddamar da littafinsa, ya fadi haka, cewa duk wanda ya yi masa wani laifi ko ba daidai ba shi ya yafe masa. Kafin ya bar duniya ya yafe wa kowa da kowa. Wasiyyarsa a wurinmu daya ce, inda za a binne shi kuma mun cika masa burinsa, duk da cewa Sarkin Musulmi ya nemi a yi masa kabari a Hubbare.