Majalisar Wakilai ta jaddada kiranta ga Shugaba Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaro, sakamakon harin ‘yan Boko Haram a kan Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Ndudi Elumelu, ya ce lokaci ya yi Buhari ya aiwatar da matsayar Majalisun Tarayya cewa ya tisa keyar manyan hafsoshin saboda sun gaza.
“Mu ‘yan adawa na kan bakarmu cewa Shugaba Buhari ya mutunta matsayar Majalisun Tarayya ya sauya manyan hafsoshin tsaron ya kawo sabbin da za su tunkari matsalar tsaron da ke addabar kasarmu”, inji shi.
Elumelu ya bayyana kaduwa da harin mayakan a kan ayarin motocin gwamnan, yana mai cewa wajibi ne a gaggauta sauya shugabancin rundunar tsaron Najeriya.
Yin hakan a cewarsa shi ne zai taimaka a magance matsalar tsaron Najeriya yadda ya kamata.
Elumelu ya ce sabbin manyan hafsoshin tsaro za su kawo sabbin dabaru da karin himma wajen kawar da matsalar.
A ranar Laraba mayakan Boko Haram suka kai wa gwamnan hari a hanyarsa ta kai wa ‘yan gudun hijira abinci.
Karo na biyu ke nan da kungiyar ta yi yunkurin kai masa har, lamarin da ya kara fusata shi.
Ya sha kalubalantar sojoji kan gazawarsu wajen kawo karshen hare-haren kungiyar a jihar.
Ko a ranar Alhamis harin da Boko Haram ta kai da rokoki a Maiduguri ya kashe mutum hudu, wasu da dama kuma suka jikkata.