✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lokaci ya yi da za a sako mana sauran mutanenmu

Mai yiwuwa mai karatu ya zuwa lokacin da ka ke karanta wannan makala, ana can ana ci gaba da tsare mutanen Aarewacin kasar nan 342,…

Mai yiwuwa mai karatu ya zuwa lokacin da ka ke karanta wannan makala, ana can ana ci gaba da tsare mutanen Aarewacin kasar nan 342, daga cikin 486, da jami`an sojoji suka kama yau kusan makonni uku a Aba ta Jihar Abiya da ke gabashin kasar nan da talatainin dare, akan hanyarsu ta zuwa Fatakwal babban birnin jihar Ribas, bisa zargin `yan kungiyar Boko Haram ne, wadanda daga cikinsu zuwa yanzu an sako mutane 144, wadanda kuma aka taso keyarsu wajen maido su arewa, inda ake sa ran zuwa yanzu kowanensu ya sadu da iyalensa a haifarsa.
Mutane 486, an ce sun fito daga jihohin Kano da Jigawa da Taraba, wai an kamasu ne a cikin jerin gwanon motoci kirar Bus-bus, har 35, akan hanyarsu ta zuwa birnin Fatakwal  da sunan cirani, kuma wai a cikinsu an samu wani kasurgumin dan ta`adda da jami`an tsaro suka dade suna nema akan ayyukan ta`addanci tun a shekarar 2007. Kai ka ji mai karatu wai tun a shekarar 2007, a lokacin da ma gwagwarmayar `yan kungiyar ta Boko Haram ba a ma santa ba a kasar nan. Ai kowa ya sa ni a kasar nan, cewa shi kanshi rikicin Boko Haram bai kankama ba sai a shekarar 2010, shekara daya, bayan an fara rikici da `yan kungiyar a Maiduguri babban birnin Jihar Barno, a bayan kishan gillar da jami`an ’yan sanda suka yi wa shugaban gwagwarmayar Malam Mahammadu Yusuf, duk kuwa da ana cikin rikicin sojojin da suka kama shi, sun mika shi ga rundunar `yan sandan jihar da ransa a shekarar ta 2009.
To, jeka ma zargin da jami`an tsaron suka yi na cewa wadancan mutane 486, `yan kungiyar ta Boko Haram ne, amma ni ina ji a cikin shekaru hudu cif-cif da ake ta wannan dauki ba dadi tsakanin jami`an tsaron kasar nan da `yn kungiyar, ya ci a ce zuwa yanzu jami`an tsaron sun san irin bayanan zarge-zarge da za su rika fada wa mutanen kasa akan su ne ne `yan kungiyar da kuma irin aikace-aikacensu  da ma irin yadda suke tafiye-tafiyensu dare ko rana daga wuri zuwa wuri da irin ababen hawa da makaman da suke amfani da su. Idan ba raina hankalin `yan kasa ba, yaya jami`an tsaro za su ce da mu, wai a cikin jerin gwanon motoci, kuma da tsakar dare suka kama su, tamfar mata, ai su jami`an tsaro sun kwana da sanin cewa da ainahin `yan kungiyar ta Boko Haram suka kama, da labarin da za su bayar tilas ya sha bamban da wanda suke bayarwa yanzu, don kuwa ko ba komai dole ya fara da cewa “Bayan wani dauki ba dadi da aka yi tsakar daren rana kaza da muka yi da `yan kungiyar Boko Haram a wuri kaza, mun samu kashe `yan kungiyar kaza, mun kuma samu makamai iri kaza-kaza daga wurinsu.” Koda kuwa ba su ce sun yi asarar mutanensu kaza ba.
Abin mamaki ko mu ce abin ban takaici, har yanzu jami`an tsaron ba su fadi komaie ba da zai kawar da shakkun da`yan kasa masu aiki da hankali akan cewa mutanen can da suka kama, `yan kungiyar Boko Haram ne, bayan ma kara jefa `yan kasa cikin shakku da bayanan nasu suka yi, sun kuma kara tona asirin jami`an tsaron kasar nan akan rashin iya aiki, kuma koda sun iya aikin, to suna yin shi ne don kawai su fararta wa gwamnatin tarayya, amma ba don yinsa cikin gaskiya da adalci ba, kamar yadda tsarin aiki da zamantakewa ya tanada.
Bayan kama wadancan mutane, wasu shugabannin al`ummar musulmi `yan Arewa mazauna kudancin, sun yi ta maza sun je Aba din inda ake tsare da mutanen, don bin ba`asin maganar, amma dai karshe tsare su aka yi. Shi kanshi karfafan ayarin da gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso ya tura, (wanda shi kadai ne daga cikin gwamnoni uku da mutanen suka fito daga jihohinsu ya tura jami`an gwamnatinsa) a karkashin jagorancin Kwamishinan ayyuka na musamman Birgediya Janar Bello Danbazau mai ritaya, suma `yan Kwamitin ba su samu ganawa da `yan asalin jihar Kanon ba, amma kuma  su, ba a tsare kowa daga cikinsu ba, mai yiwuwa ko dan shugaban kwamitin hafsan soja ne?.
Duk da yake Majalisar koli ta harkokin addinin Musulmi da al`ummar Musulmi da wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama daga sassa daban-daban na kasar nan sun nisanta mutanen da aka kama din da cewa ba `yan kungiyar Boko Haram ba ne, har sai da ta kai Mataimakin Shugaban kungiyar Jama`atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Abubakar Orlu, ya fada wa duniya a Fatakwal cewar wasu daga cikin wadanda aka kama din `yan hayarsa ne a Fatakwal sama da shekaru 20. Amma dai wadannan kiraye-kiraye ba su sa gwamnatin tarayya ta saurara ba, bare ta sako wadanda take tsare da su din.
Bayan kama wadannan mutane, sai kuma ga labari daga jami`an tsaro na an sake kama wasu mutane 50, musulmi `yan Arewa a cikin wata Bus ta kamfanin Young Shall Grow a Enugu da ake zargin `yan kungiyar ta Boko Haram ne, a takaice ta kai yanzu a kusan dukkan jihohin kasar har da na wasu jihohin Arewa, inda duk aka ga dan Arewa Bahause, dan Boko Haram ake kiransa.
A gefe daya shi kuma gwamnan Jihar Imo, Cif Rochas Okorachas, gwamnan da yake alfahari da al`ummar Hausa, akan sun yi masa sha-tara ta arziki, yake kuma Hausa kamar jakin Kano, da rana tsaka ya bullo da shirin a yi rijistar dukkan wani dan Arewa da yake zaune a jihar, wai da sunan matakan tsaro, kai ka ji mai karatu wannan cin kashi, duk da sunan Boko Haram ya bulla a Arewa. A zaman kaucewa irin abin da ka biyo baya ga sauran kabilun kasar nan dake zaune arewa, an ji Sarkin `yan kabilar Ibo mazauna jihar Kano Cif Boniface Ebekwe, yana yintir da alla-wadai da yin waccan rijista wadda ya ce bata dace ba, sannan ya nemi mahukuntar jihar ta Imo da su gagauta dakatar da shirin, yana mai nuni da cewa su da suke zaune Arewa ba wanda ya ce zai tantancesu bare batun a yi masu rijista ya taso.
Da wannan danbarwa, ina ga lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta tsawata wa jami`an tsaronta da su daina irin wadancan takale-takale, ta mayar da hankali akan dukkan abin da zai kawo rashin zaman lafiyar da kasar nan take ciki, sannan kuma ta gaggauta sako sauran `yan Arewa 342, da take tsare da su. Ga sauran mahukuntan jihohi da al`ummominsu ya kamata su rika la`akari da yadda Allah Ya hada zamantakewar kasar nan, su daina neman tada husuwar da za ta wargaza kan kasar, zamantakewar da kowane bangare ke bukatar kowa don ci gaba da karuwar arziki.