✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LMC ta ci tarar Remo Stars Naira miliyan 6

Kwamitin Shirya Gasar Rukuni-Rukuni na Najeriya (LMC) ya ci  kulob din Remo Stars da ke Shagamu a Jihar Ondo tarar Naira miliyan 6 saboda laifin…

Kwamitin Shirya Gasar Rukuni-Rukuni na Najeriya (LMC) ya ci  kulob din Remo Stars da ke Shagamu a Jihar Ondo tarar Naira miliyan 6 saboda laifin yi wa alkalin wasa rashin da’a a ranar Lahadin da ta gabata.  Kwamitin ya sake cin tarar Shugaban kulob din Kunle Soname tarar Naira miliyan 1 saboda amincewarsa a kan yadda ’yan kwallon suka nuna rashin da’a a kan alkalin wasan a lokacin da ya yi hira da manema labarai.  Haka kwamitin ya dage Manajan Kulob din shiga harkokin wasanni daga yanzu har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Sannan kwamitin ya mayar da kulob din yin wasanninsa na gida a garin Osogbo na Jihar Osun har sau uku.

Kwamitin ya dauki wadannan matakai ne bayan ya yi nazari a wasan da Remo Stars ta yi da kulob din Bendel Insurance a gasar rukunin Firimiya ta Najeriya bayan an tashi wasan da ci 1-1.

Ana gab da tashi wasan ne kulob din Remo Stars ya zura kwallo ta biyu a raga amma alkalin wasan ya ce an yi satar fage, wanda hakan ya harzuka ’yan kwallon  da magoya bayansu inda suka yi ca a kansa suna antaya masa bakaken maganganu.

Kwamitin ya ce ya yi haka ne don ya zama darasi ga sauran kulob din da ke fafatawa a wannan gasa.

Kawo yanzu dai an yi wasanni hudu a wannan gasa, inda ake sa ran yin na biyar a jibi Lahadi.