Ba tun yau ba ake muhawara a kan dacewa ko rashin dacewar salon da marubutan Hausa suka dauka wajen wallafa kirkirarun labarai, inda aka yi ta kukan cewa marubutan sun fi ta’allaka wajen rubutu a kan soyayya, suka banzatar da sauran maudu’ai, kamar na siyasa, zamantakewar al’umma, tarihi, rayuwar yau da kullum da sauransu.
Irin wannan takaddama ta taba yin zafi a shekarun da suka gabata, inda har Gwamnatin Jihar Kano, karkashin mulkin Gwamna Ibrahim Shekarau ta gudanar da wani kwarya-kwaryan bikin kona irin wadannan littatafai da ake wa lakabi da ‘Adabin Kasuwar Kano.’
A makon nan ne ma wasu marubuta suka sake bijiro da irin wannan muhawara, inda marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran rayuwa, Malam Auwal G. danbarno ya kalubalanci marubutan Hausa da cewa ya kamata su canza alkibla, su dawo daga rakiyar rubutu kan soyayya. Maimakon haka, ya nemi da su dukufa wajen rubuce-rubuce da suka shafi siyasa, kasuwanci, tarihi, kimiyya da sauransu.
A wata mukala da ya rubuta mai taken ‘Zuwa Ga Abu Hidaya’ ya ce: “Abin da na fada shi ne, muna da marubuta akalla wajen mutum dari biyu. A cikin mutum dari biyu, akalla wajen dari da hamsin duk suna rubutu ne bisa abin da ya shafi soyayya. Ganin yanayin halin da muke ciki na tabarbarewar tsaro a Arewa, da yadda ’yan Kudu ke cin mu da yakin biro, na yi tunanin ya kamata marubutanmu su karkatar ta akalar rubutunsu zuwa ga tsantsar abin da ya shafi matsalolin da muke ciki, maimakon mu tsaya lissafin yarinyar fara ce doguwa mai duwawuka manya.”
Ya ci gaba da cewa: “Na fadi cewa, a yayin da ake kashe mana ’yan uwa, ana sace mana ’ya’ya, bai kamata mu tsaya muna wani rubutu ‘wance ta yaudari wane’ ba. Ita kanta soyayyar, idan babu kwanciyar hankali ba ta yiwuwa. Shin wa ke ta littafi a garin da ake yaki, balle ma wani littafin soyayya? Na kawo misali da bayan gama yakin basasar Najeriya, yadda sojojin Kudu suka yi ta rubuce-rubuce da bayyana ra’ayoyinsu da kissima karya a ciki, suna fadin yadda aka keta musu ’yanci. Na kawo misalin littafin The Nagerian Rebolution and Biafran Cibil War, wanda Kwamandan Rundunar Sojojin Biyafara ya rubuta da hannunsa. Sai littafin Obasanjo My Command, wanda shi ma ya rubuta da hannunsa da kuma littafin Chukwuma Kaduna Nzegwu. Sai littafin The Broken Bridge, na wani likita Bayarabe da kuma The Tragedy of the bictory na Kwamanda Alabi Isiama. Wadannan duk sun bayyana yadda suka so a littafin, idan ka dauke littafin Alabi Isiama da ke dauke da kaso saba’in na sahihan labari.”
Haka kuma ya karkare da cewa: “Na ce marubutanmu su mayar da hankali wajen kawo tarihin iyaye da kakanninmu da suka yi gwagwarmaya a baya, domin ’ya’ya da jikokinmu su sami abin koyi.”
Rabi’u Muhammad, wanda aka fi sani da lakanin Abu Hidaya, wanda shi ma marubucin Hausa ne kuma mai sharhi kana bin da ya shafi al’amuran al’umma, ya mayar da martanin cewa: “Da kake maganar wai lokaci ya yi da za mu daina rubutu a kan fara doguwa da makamantansu, ai wannan ba shi ne matsalar ba. Matsalar ita ce a ce ka gama littafi tsaf ba darasi, wanda ake yi wa littafan ba ya wannan kallon amma idan ka koma baya cikin labaran tarihi, labaran soyayya sun fi shahara, irin na su Mujisu da Barira kuma su wadannan labarai suna nuna mana illar kiyayya ne da kuma auren wanda ba ya son ka. Haka labarin Laila Majnun, shi ma yana nuna mana illar cin amana. Har ila yau, mafi yawa daga cikin labaran suna nuna tausayi gami da wayar da kan jama’a zuwa ga samar da al’umma ta gari. Kuma a cikin wadannan littattafan da kake Magana, akwai yadda ake koyar da zamantakewa da hanyar dogaro da kai, kimiyya da fasaha. Kuma yawanci kowane mutum soyayya ce jigon samuwarsa, sannan dukkan zuciya tana son jin dadadan kalamai cikin yabonta, wanda kuma rubutu a wannan fagen yana kara samar da ci gaba a nan.”
Ya ci gaba da cewa: “Idan ka ce a bar wannan bigire a koma rubutu a fagen yaki da makomar kasa, ai sai in ce maka duk wanda ya yi haka ya bata wa kansa lokaci; domin matsalar kasa musamman Najeriya shi ne munafunci da rashin son juna. Kuma mutane da yawa sun rubuta wani abu game da haka amma har yanzu jiya-i-yau, ba abin da ya canja. Ka ga kuwa a fagen soyayya mutane da yawa sun karu, musamman wajen sanin wa ke son ka tsakani da Allah kuma wa ya kamata ka aura.”
Daga dukkan alamu dai, za a ci gaba da tafka muhawara a kan wannan batu, musamman ma ganin yadda al’amuran fina-finan Hausa na neman danne harkar rubutun littattafan kirkirarrun labarai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan takaddama na iya kawo sauyin akalar marubutan? Lokaci ne zai iya tabbatar mana.
Littattafan Hausa: Takaddama tsakanin Auwal G. danbarno da Abu Hidaya
Ba tun yau ba ake muhawara a kan dacewa ko rashin dacewar salon da marubutan Hausa suka dauka wajen wallafa kirkirarun labarai, inda aka yi…