Littattafai 400 ne suka fafata a gasar littattafan da Jami’ar Edinburgh da ke Birtaniya ta shirya.
An kafa jami’ar ne a shekarar 1583, ta kuma ta fara shirya gasar littattafan ne a shekarar 1919, bayan Janet Coats matar marigayi mawallafi James Black ta bukaci a kirkiro wannan gasar..
Jama’a ne suke shigar da littattafan da za su fafata duk shekara, inda malamai da manazarta da kuma masana harkar adabi ke karanta littattafan don fitar da gwarzon littafi na shekara.
Fitaccen dan jarida Sally Manusson ne ya sanar da sunan marubuci Jim Crace da kuma marubuciya Hermione Lee ne suka lashe gasar ta bana.
An sanar da sunan wadanda suka yi nasarar ne a ranar Talata yayin bikin littattafai na duniya da Jami’ar Edinburgh ta dauki nauyi.
Sauran wadanda suka samu nasara sun hada da marubuci DH Lawrence da Graham Greene da Angela Carter da kuma Ian McEwan, inda aka ba kowane daga cikinsu Fam dubu 10 (daidai da Naira miliyan 2 da dubu 600 da dari 4).
Tsohon dan jarida Jim Crace ya lashe gwarzon marubuci a bangaren labaran kirkira da littafinsa mai suna ‘Harbest’.
Marubucin dan kasar Birtaniya wanda ya rubuta littattafai sama da 13 ya kuma zama gwarzon marubuci na Jami’ar Yale.
Littafin ‘Harbest’ yana ba da labarin wani kauye ne a Birtaniya da aka rika rikicin mallakar filaye, wanda a da ba dauki fili wani abu ba.
daya daga cikin alkalan gasar a fannin labaran kirkira Dokta Lee Spinks ya ce: “Littafin ‘Harbest’ na Jim Crace ya zo da salon yadda ake gado a al’adance da kuma rawar da kowane muhalli yake takawa don neman ci gaba.”
Farfesa Dame Hermione Lee ce ta zama gwarzuwar marubuciya a bangaren litttafan tarihin mashahurin mutum.
A shekarar 2013 aka kirkiro da bangaren wasan kwaikwayo a gasar.
A bana littafin wasan kwaikwayo mai suna ‘Cannibals’, wanda dan Birtaniya Rory Mullarkey ya rubuta mai dauke da jigo a kan yake-yake lokacin rusasshiyar Tarayyar Sobiet ne ya zama zama gwarzon littafin wasan kwaikwayo.
Littattafai 400 suka fafata a ‘Gasar Littattafan Jami’ar Edinburgh’
Littattafai 400 ne suka fafata a gasar littattafan da Jami’ar Edinburgh da ke Birtaniya ta shirya.An kafa jami’ar ne a shekarar 1583, ta kuma ta…