✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littafin kasuwanci a ma’aunin nazari

Tsananin bukatar da ake da ita na ilimin kasuwanci a makarantun sakandaren kasar nan da kuma yadda aka juya akalar harkar neman ilimi tare da…

Tsananin bukatar da ake da ita na ilimin kasuwanci a makarantun sakandaren kasar nan da kuma yadda aka juya akalar harkar neman ilimi tare da koyon sana’o’i, su ne musababbin da ya janyo Chima I. Azu da abokinsa Razak Abdullahi suka rubuta littafin da suka sanya masa suna: Elementary Marketing For Senior Secondary Schools (Matakin Farko Na Lakantar Ilimin Kasuwanci Don daliban Sakandare.
Babu shakka wadanda suka rubuta littafin sun yi zurfin tunani, inda suka tsara littafin daki-daki kuma suka shirya abubuwa kamar haka: Babin gabatarwa a shafi na 1 da babin ma’anonin kasuwanci a shafi na 5 da babin rabe-raben hajoji a shafi na 7 da babin ire-iren kasuwanci a shafi na 12 da babin dabi’un abokin hulda a shafi na 14 da babin tsarin kasuwanci da bincike a shafi na 17 da babin farashi a shafi na 22 da babin tallace-tallace a shafi na 25 da kuma babin gwaji na dalibai a shafi na 39. Sai kuma bangaren tambayoyi da gwaje-gwaje kan abin da aka karanta a littafin daga shafi na 39 zuwa shafi na 50.
Wata hobbasa da marubutan suka yi, ita ce wajen ganin sun yi wa littafin dab’i mai kyau tare da sanya masa bango mai karko ta yadda duk rikon da dalibi zai yi masa ba zai yage ba. Alamar da suka sanya bangon littafin da ke nuna wasu kalmomin kasuwanci zai janyo hankulan yara su yi sha’awar littafin. Hakazalika launukan da suka sanya wa littafin sun dace da irin laununkan da yara suke so. Wani tsari da aka yi wa bangon littafin na karshe na sanya hotuna tare da tarihin marubutan ya dace kwarai da gaske.
Don haka marubutan sun cancanci jinjina saboda dagewar da suka yi wajen ganin littafin ya fito ba tare da kuskuren dab’i ko na tuntuben alkalami ba. Marubutan ba su yi gaban kansu ba wajen mamaye komai kamar yadda wasu marubuta suke yi. Sai suka raba ayyukan ga wadanda suka dace. Misali sun bai wa Nathaniel Abiodun aikin tsara bango da kuma littafin baki daya. Shi kuwa kamfanin Partners and Seed shi ne ya kula da gyare-gyaren rubutu sai kuma kamfanin bisible Brand Consult ya kula da tsarawa sannan kuma Oyeniyi Kehinde shi ne ya kula da dab’in littafin. Wannan mataki da marubutan suka dauka ya sanya littafin ya yi kyan bugu tare da samun karbuwa ga jama’a.
Hakan ya sa littafin ya zama tamkar wani mabudi na bude sabuwar manhaja ta ilimin kasuwanci a makarantun sakandare tare da cusa wa yara dalibai tunanin kasuwanci don dogaro da kansu a matakan rayuwa daban-daban. Sai dai kuma littafin ya dace da manhajar ilimin sakandare ta kasa kamar yadda Darakta a Hukumar Lura da Makarantun Sakandare ta Abuja, Misis Yelwa Fatima Baba-Ari ta bayyana a tsokacin da ta yi a cikin littafin a shafi mai lamba bi na littafin.
Daga shafi na 1 zuwa shafi na 4, marubutan sun yi bayani a kan ma’anar kasuwanci da abin da ya kunsa, inda suka ce kasuwanci wata hanya ce da daidaikun mutane ko kamfanoni suke yi don samun abin da suke bukata daga wurin jama’a. Inda a shafi na 2 suka yi bayani kan hada-hadar kasuwanci, inda suka ce ta kunshi saye da sayarwa da kudi da ajiya da zirga-zirga da aiwatarwa da asara da cin riba da kuma tattara bayanai.
Tun daga shafi na biyar zuwa na shida, marubutan sun yi bayani kan abin da kasuwanci ya kunsa sannan kuma a shafi na 7 sun yi bayani dalla-dalla kan rabe-raben haja da kuma ma’anar haja. Suka ce ita haja kan iya zama duk wani abu da za a kasa a kasuwa don janyo hankalin masu saya. Haja ta iya zama abin sanyawa ko ci ko kuma wani abin kyale-kyale. Wani abin da ya ke jan hankali shi ne a shafi na 14, inda marubutan suka yi bayani a kan dabi’un abokin hulda. Inda suka bayyana wadansu abubuwa da ke janyo hankali mai sayen kaya, wadanda suka hada da ra’ayi da al’ada da mu’amala da kuma tunani.
Wani abu da zai kara burge yara dalibai tare da janyo hankulansu kan littafin shi ne yadda marubutan suka yi amfani da hotuna wajen fasalta darasin da suke magana a kai, ta yadda yara za su samu saukin fahimtar littafin ba tare da wata matsala ba. Marubutan sun yi ta sanya hotuna tun daga shafi na uku har zuwa shafin karshe.
Marubutan sun ware shafuka na musamman inda suka yi tambayoyi don gwada yaran da suka karanta littafin. Hakan zai sa duk yaron da ya karanta littafin tuna abubuwan da ya karanta a littafin. Sai dai kuma an samu kura-kurai kadan wajen sanya lambobin littafin kamar a shafi na 49 da shafi na 50, ba su fito sosai ba. Saboda haka ya kamata mawallafan su kiyaye a bugun gaba don kada su maimaita kuskuren.