A ranar Litinin 14 ga wannan wata da ne Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) za ta gudanar da taron fidda jadawalin gasar cin Kofin Zakarun Kulob-Kulob na Turai zagaye na biyu. Za a fidda jadawalin ne da misalin karfe 12:00 na rana agogon Najeriya a hedkwatar hukumar da ke Zurich na kasar Suwizilan.
Jadawalin ya nuna za a yi amfani da tukwane biyu ne wato ta A da B inda za a ware kungiyoyi 8 da suka kasance na daya a rukunin A, yayin da daya tukunyar za ta kunshi kungiyoyin kwallon kafa 8 da suka kasance na biyu wato rukunin B.
Sannan jadawalin ya nuna babu kungiyar da za ta hadu da ’yar uwarta da suka fafata a zagayen farko a wannan mataki, ma’ana idan kungiyoyin sun hadu a rukunin da aka kasafta su a zagayen farko, to ba za su sake haduwa a wannan zagaye na biyu na wannan mataki ba.
kungiyoyin da suka kasance na farko a zagayen farko kuma wadanda za su kasance a tukunyar A sun hada da Real Madrid daga Sifen da Wolfsburg daga Jamus da Atletico Madrid daga Sifen da Manchester City daga Ingila da FC Barcelona daga Sifen da Bayern Munich daga Jamus da Chelsea daga Ingila da kuma Zenith daga Rasha.
kungiyoyin da suka kasance na biyu a zagayen farko kuma wadanda za su kasance a tukunyar B sun hada da Paris Saint Germain daga Faransa da PSb daga Holland da Benfica daga Portugal da Jubentus daga Italiya da Roma daga Italiya da Arsenal daga Ingila da Dynamo Kyib daga Ukraine daga kuma Gent daga Beljiyum.
Bayan an kammala jadawalin, za a gudanar da wasannin farko ne a ranakun 16 da 17 da kuma 23 da 24 na watan Fabrairun badi yayin da za a gudanar da wasa zagaye na biyu a ranakun 8 da 9 da kuma 15 da 16 ga watan Maris din badi.
Sannan za a sake jadawalin matakin kwata-fainal ne a ranar 18 ga watan Maris, 2016 da misalin karfe 12:00 na rana agogon Najeriya yayin da za a yi jadawalin wasan kusa da na karshe a ranar 15 ga Afrilun 2016 da misalin karfe 12:00 agogon Najeriya.
Kulob din FC Barcelona na Sifen ne dai yake rike da kofin bayan ya lallasa na Jubentus da ke Italiya da ci 3-1 a wasan karshe.
Litinin za a fidda jadawalin zagaye na biyu na gasar Zakarun Turai
A ranar Litinin 14 ga wannan wata da ne Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) za ta gudanar da taron fidda jadawalin gasar cin…