✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Litar fetur za ta koma Naira 97 a badi – Gwamnati

A ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin fara janye tallafin man fetur daga shekara mai zuwa.Minista a Ma’aikatar Albarkatun…

A ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin fara janye tallafin man fetur daga shekara mai zuwa.
Minista a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Dokta Ibe Kachukwu ne ya sanar da haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin hadaka na majalisun dokokin kasar nan domin ya kare kasafin kudin ma’akatarsa.
Minista Kashukwu ya ce  a bana an kashe fiye da Naira tiriliyan daya kan tallafin mai, kuma wannan “dawainiya ce da gwamnatin ba za ta iya ci gaba da dauka ba,” inji shi.
Ministan ya ce za a janye tallafin da kadan-kadan, inda da farko za a kara kudin mai ya koma Naira 97 kowace lita daga Naira 87  a kan kowace lita a yanzu.
Masana harkokin tattalin arziki a kasar nan da kasashen ketare sun dade suna kira ga gwamnatin ta janye tallafin man fetur saboda a cewarsu dawainiyarsa ta fi alfanunsa yawa.
A makon jiya ne Bankin Duniya ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa gwamnatin Najeriya ta janye tallafin mai. Bankin ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya fitar a kan tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce ana bukatar samun wani sarari ta fuskar kudin shiga domin, kasar ta samu damar sararawa ta samar da muhimman abubuwan da ake bukata.