✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun raba tagwaye manne da juna a Bauchi

Likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH)da ke Bauchi sun yi nasarar raba jarirai biyu ’yan tagwaye da aka haife su a…

Likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH)da ke Bauchi sun yi nasarar raba jarirai biyu ’yan tagwaye da aka haife su a manne da juna.

Wannan shi ne karo na biyu da kwararrun likitocin asibitin suka samu nasarar raba tagwayen da aka haife su manne da juna.

Jaririn da likitocin suka raba a asibitin, an haife shi ne mutum amma da tsiron wani dan Adam da ke manne a jikinsa. Kuma tsiron jikin daya ba ya da rai sai suka zama kamar tagwaye manne da juna.

Wannan jariri mai suna Abubakar Sani ya fito ne daga garin Azare da ke Karamar Hukumar Katagum da ke Jihar Bauchi. Bayan da aka haife shi sai iyayensa suka kai shi Babban Asibitin Tarayya da ke Azare daga bisani aka dawo da su Bauchi, inda aka yi nasarar cire tsiron halittar mutum da ke manne a jikinsa.

Lokacin da aka kawo shi Asibitin ATBUTH da ke Bauchi, likitoci sun yi masa gwaje-gwaje daban-daban, kafin daga bisani aka yi masa aiki, a cire tsiron.

Kwararrun likitocin da suka yi aikin a karkashin jagorancin Dokta Kefas J. Bwala, sun ce shi wannan jaririn abin da ya tsiro a jikinsa na halittar dan Adam shi ma tagwaye ne kuma ba lallai ne ya zama yana da rai ba.

An shigar da Abubakar dakin fida da misalin karfe 9:20 na ranar Alhamis din makon jiya kuma aka fito da shi da misalin karfe 12 da minti 50. Kuma likitocin sun fito suna murmushi, alamar da ke nuna cewa sun yi nasarar  aikin da suka gudanar.

Dokta Kefas Bwala ya ce sun samu nasarar raba su kuma ana sa ran  jariri Abubakar zai samu sauki cikin kwana goma kuma a halin yanzu yana wajen da ake kula da majinyata da ciwonsu ya tsananta amma yana cikin hayyacinsa.

Iyayen yaron sun ce sun bar wa Allah komai kuma sun dukufa ne da yin addu’o’in Allah Ya sa a sam,u nasarar aikin har zuwa lokacin da aka fito da shi.

Wannan ne raba tagwaye manne da juna na biyu da likitoci suka yi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.