✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sace Dokta Ganiyat: Likitoci sun janye yakin aiki

Ƙungiyar kikitoci ta NARD ta janye yajin aikin da ta shiga kan Dokta Ganiyat Poopola da aka yi garkuwa da ita

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta janye yajin aikin da ta shiga kan yin garkuwa da ɗaya daga cikin ’ya’yanta, Dokta Ganiyat Poopola.

Ƙungiyar ta sanar cewa mambobinta za su koma bakin aiki ne daga ƙarfe 8 na safiyar Litinin, mako guda bayan ta fara shi.

Ta bayyana cewa nan da mako uku masu zuwa Kwamitin Zartarwata (NEC) zai sake zama domin tattaunawa a game da lamarin.

Sanarwar da NARD ta fitar ɗauke da sa hannun shugabanta, Dokta Dele Abdullahi Olaitan, da aakatarenta, Dokta Ondoaka Christopher Obinna, ta ce sun janye yajin aikin ne sakamakon yadda suka lura hukumomin gwamnati sun duƙufa wajen ganin an ceto Dokta Ganiyat Poopola.

Sun kuma yaba da yadda kafofin watsa labarai da sauran al’umma suka nuna damuwa game da halin da likitar take ciki.

Wata takwas ke nan da ’yan bindiga suke tsare da Dokar Ganiyat Poopola bayan sun yi garkuwa da ita tare da mijinta da ɗan ɗan uwansa a gidanta a Jihar Kaduna a watan Dimaban 2023.

Daga bisani  a watan Maris, 2024, sun sako mijin nata, Squadron Leader, Nuruddeen Poopola, amma suka ci gaba da riƙe Doka Gajiyar tare da ɗan nasu.