✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Likitoci 9,000 sun bar Najeriya cikin shekara 2’

Shugaban kungiyar NMA na kasa,  Farfesa Innocent Ujah, ne ya bayyana hakan

Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta ce likitoci ’yan Najeriya sama da 9,000 ne suka bar Najeriya zuwa wasu kasashen tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018.

Kungiyar ta ce kasashen da mambobin nata suka fi zuwa don neman rayuwa mafi inganci sun hada da Amurka da Kanada da kuma Birtaniya.

Shugaban kungiyar na kasa,  Farfesa Innocent Ujah, ne ya bayyana hakan yayin wani taron gabatar da makaloli na kungiyar da ya gudana a Abuja ranar Litinin.

Taken taron na bana dai shi ne: “Yin hijirar likitoci da zuwa ketare neman lafiya: Tagwayen bala’o’in da ke tunkarar Najeriya.”

Farfesa Innocent ya ce yin kaurar likitocin ya sa an bar Najeriya da kaso 4.7 cikin 100 na kwararrun ma’aikatan lafiya suna duba jama’a, inda ya ce hakan ba alheri ba ne gareta.

Ya ce, “Yin hijirar likitoci yana kara dankwafar da harkar lafiyar Najeriya wacce dama take cikin halin ni-’ya-su, sannan yana kara gibin ci gaba tsakaninta da takwarorinta a fannin lafiya.

“Galibi ma’aikatan lafiya kan yi kaura ne daga kasashe masu tasowa zuwa wadanda suka ci gaba, inda suke barin kasashen nasu, wadanda su ne suka fi bukata cikin mawuyacin hali,” inji shi.

Shugaban ya kuma kawo alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), wacce ta bukaci likita daya ya rika duba mutum 4,000 zuwa 5,000, a maimakon likita daya ga mutum 60 da hukumar ta bukata.

Ya kara da cewa zuwa kasashen ketare don neman lafiya ma ba karamin kalubale na ne ga harkar lafiyar kasar.

Sai dai da yake nasa jawabin yayin taron, Minista a Ma’aikatar Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dukufa matuka wajen gyara harkar lafiya da kuma magance kalubalen da ke addabarta.

Shi kuwa tsohon Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole, ya zargi rashawa da cewa ita ce ummul-aba’isun matsalolin kasar.