✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitan Najeriya 1 na kula da majinyata 2,753 – Gwamnati Tarayya

Shugaban sashen ma’aikatan lafiya na ma’aikatar lafiya ta kasa, Shakuri Kadiri ya bayyana cewa, karancin likitoci a Najeriya yasa likita daya yana kulawa da majinyata…

Shugaban sashen ma’aikatan lafiya na ma’aikatar lafiya ta kasa, Shakuri Kadiri ya bayyana cewa, karancin likitoci a Najeriya yasa likita daya yana kulawa da majinyata dubu 2,753.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, a yayin kaddamar da kundin karfin ma’aikatar lafiya na shekara ta 2018 da kuma mika rajista na ma’aikatan lafiya ta Najeriya a hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya da sauran masu fada aji.

Shakuri, ya ce kundin yana dauke da jimillar tabbatattun likitoci ta Najeriya inda ya bayyana cewa gaba dayansu su dubu 74,543 ne. Ya yi nuni da cewa, hakan na nufin likitoci 36.3 suke kulawa da mutane dubu 100 a kasar. Tun dai a shekara ta 2012, ba a sake tattara kundin da zai nuna yawan likitoci masu kulawa da majinyata a kasar ba.

Shugaban ofishin hukumar lafiya ta duniya da ke Najeriya, Clement Peter, ya ce kundin zai tabbatar da cewa an samar da bayanai da zasu taimaka wajen tsare-tsare da kuma gudanar da harkokin kula da lafiya a kasar.

Ya ce, hukumar lafiyar ta duniya tare da kudade daga hannun gwamnatin kasar Canada ce, ta gina samfurin kundin da kuma rajistar bayanan ma’aikatan lafiyan.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, kundin yana dauke da bayanan ma’aikatan lafiya na jihohi 10 inda ya jaddada bukatar gwamnatin tarayya da sauran masu fada aji da su fadada kundin saboda shigar da sauran jihohin kasar, hukumomi na gwamnatin tarayya da ma masu zaman kansu.

Ministan lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire, ya ce tuni gwamnati ta dukufa wajen tattaro bayanai akan ma’aikatar lafiya a fadin kasar saboda inganta tsare-tsare da gudanarwar ma’aikatan domin samar da ingantaccen kulawa da lafiyar ‘yan kasa.