✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Likita ya yi wa matarsa dukan kawo wuka a Kalaba a kan yi wa ’yarsu kaciya

Mutumin dai ya tsaya kai da fata a kan sai an yi wa ’yar tasu kaciya.

Wani likita mai suna Ikari Jolly da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba ya yi wa matarsa Naomi Jolly, dukan kawo wuka sakamakon ta ki amincewa da umarnin yi wa ’yarsu mai suna Amanda kaciya.

Yi wa mata kaciya a Jihar Kuros Riba tsohuwar al’ada ce da har yanzu wasu iyalan ke yin ta na yi wa ’ya mace kaciya, duk kuwa da kokarin hana yin hakan da kungiyoyi da ke fafutukar hana cin zarafin mata da kananan yara ke yi.

Wannan matsala tsakanin matar da mijinta na dukan ta da yake yi kamar yadda Aminiya ta samu labari daga
makwabcin likitan ya bukaci a sakaya sunanta ta ce, tun da suka yi aure a 2015 abu kankani sai ya rika dukan matar.

Musabbabin dukan kamar yadda Naomi ta shaida wa wakilinmu inda ta ce, “Sai an yi wa ’yarmu Naomi mai shekara biyar kaciya, ni kuma na ki amincewa da yin hakan, tun daga nan muka fara takun saka da shi, saboda naki yi mata kaciya.” Inji ta.

Da wakilinmu ya tambaye ta ko me ya sa kika ki amincewa da bin umarnin ki yi kaciyar don ki samu zaman lafiya? Sai
Naomi ta ce, “Nima iyayena sun yi mini kaciyar ina karama ’yar shekara 12 na ga irin jinin da ya zuba daga jikina kamar ba zan rayu ba, shi ya sa na ki tun daga nan abu kadan sai ya hau dukana ya farfasa min jiki.”

Naomi Jolly ta kara da cewa, “Lokacin da yarinyar ta cika shekara daya da haihuwa na ce masa mu yi mata bikin
zagayowar ranar haihuwarta shekara daya, ya ce ba zai yi ba, sai na ganganda na hada kayan biki. Ganin haka sai ya
zo ya watsar da duk abin da ke kan teburin da kyar na kwaci kaina, na gudu na tafi Abuja ya biyo ni na dawo. Duk da haka wulakanci da duka bai canja ba, na sake gudu na tafi Legas da ’yan uwansa suka samu labarin inda nake suka zo aka sake tafiya da ni za su kwace ’yar
tamu na hakura na dawo to shi ne ka kin yi mata kaciya hakan ya faru gare ni.” Inji ta.

Aminiya ta ji ta bakin maigidan mijin Naomi kan ko mai ya sanya bai sanya hikima da lallashin matarsa ba, har ya
shawo kanta a yi abin da yake so mai makon dukanta? Sai ya ce, “Yi wa mata kaciya al’adar gidanmu ce. Don haka, dole a yi wa ’yata kuma sai an yi.” Inji shi.

Yanzu haka magana na gaban Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba sashen binciken masu aikata miyagun laifuka ana bincike.

Kazalika, DSP Ajala Benjamin na sashen binciken ya tabbatar wa wakilinmu rahotan kuma ana nan ana ci gaba da yin bincike.