Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta ce karancin likitocin da ake fuskanta a kasar ya yi munin da a yanzu likita daya ne ke duba marasa lafiya 10,000.
Kungiyar ta ce a halin da ake ciki, likitocin da ake da su a fadin kasar ba su wuce 10,000 ba.
- NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
- An kwace bindigogi 5 daga hannun wadanda ake zargi da kai hare-hare a Osun
Ta ce adadin likitocin raguwa yake kullum sakamakon barin kasar da suke yi zuwa aiki a kasashen waje.
Shugaban kungiyar na kasa, Dokta Emeka Orji, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da jaridar Punch ranar Litinin.
A cewarsa, kimanin likitoci 100 ne ke barin kasar zuwa ketare duk wata don neman aiki.
Ya ce, daga cikin likitoci 80,000 da suka yi rajista, kimanin kaso 64 cikin 100 ba sa aiki saboda wasunsu sun yi murabus, wasu sun bar kasar, wasu sun sake aiki, wasu kuma sun mutu.
Shugaban ya kuma ce kafin wannan lokacin, “Likitoci 16,000 ake da su, amma yanzu ba su wuce dubu tara zuwa 10 ba.”
Hakan na nufin likitocin da ake da su da za su kula da al’ummar Najeriya su sama da miliyan 200, ba su wuce guda 10,000 ba.