✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Libya ta yanke wa mayakan IS 23 hukuncin kisa

Kotun Daukaka Kara a kasar Libiya ta yanke hukuncin kisa a kan wasu ’yan kungiyar IS mutum 23 bisa kama su da laifi kaddamar da…

Kotun Daukaka Kara a kasar Libiya ta yanke hukuncin kisa a kan wasu ’yan kungiyar IS mutum 23 bisa kama su da laifi kaddamar da wasu munanan hare-hare a shekarun baya a kasar.

Kotun wacce ta yi zamanta a birnin Misrata ta kuma yanke wa wasu mutum 14 hukuncin daurin rai da rai, yayin da wasu karin mutanen 9 suka sami hukuncin tsakanin shekaru 3 zuwa 12.

Tun bayan rikicin shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyar kifar da gwammantin Muammar Gaddafi, kungiyoyin IS da wasu masu tsatsauran ra’ayin addini suka karbe iko da birnin Sirte, wanda ke zama mahaifa ga tsohon shugaban.

Daruruwan ’yan kungiyar ta IS na kulle a kurkuku tun bayan da asojojin gwamnati suka ci karfinsu, inda da damansu ke jiran shari’a.