Kotun Daukaka Kara a kasar Libiya ta yanke hukuncin kisa a kan wasu ’yan kungiyar IS mutum 23 bisa kama su da laifi kaddamar da wasu munanan hare-hare a shekarun baya a kasar.
Kotun wacce ta yi zamanta a birnin Misrata ta kuma yanke wa wasu mutum 14 hukuncin daurin rai da rai, yayin da wasu karin mutanen 9 suka sami hukuncin tsakanin shekaru 3 zuwa 12.
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur?
- An kashe ’yan ta’addan ISWAP 3 a Borno
Tun bayan rikicin shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyar kifar da gwammantin Muammar Gaddafi, kungiyoyin IS da wasu masu tsatsauran ra’ayin addini suka karbe iko da birnin Sirte, wanda ke zama mahaifa ga tsohon shugaban.
Daruruwan ’yan kungiyar ta IS na kulle a kurkuku tun bayan da asojojin gwamnati suka ci karfinsu, inda da damansu ke jiran shari’a.