Wata kotu a kasar Libiya ta amince dan tsohon shugaban kasar marigayi Ma’amar Ghaddafi, Saif al Islam, ya tsaya takarar shugaban kasa bayan hukumar zaben kasar ta soke takararsa ta neman kujerar.
Yanzu haka dai Saif al Islam zai ci gaba da kasancewa a cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaben da za a gudanar a ranar 24 ga wata Disamba 2021.
- Taliban ta haramta yi wa mata auren dole a Afghanistan
- ’Yan bindiga sun kashe tsohon Kansila sun sace direbobin Dangote a Zariya
Kotun Daukaka Karar da ke birnin Sabaha a yankin Kudancin kasar ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a.
Said al Islam ya daukaka karar ce yana kalubalantar matakin soke takararsa da hukumar zaben ta yi, bisa abin da hukumar ta kira rashin dacewa a karkashin dokar kasar.
Saif al Islam Gaddafi, mai shekara 49, a shekarar 2015 an taba yanke masa hukuncin kisa, kafin daga bisani gwamnatin kasar ta yafe masa.
Ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara ne a watan Nuwambar da ta gabata, amma hukumar zaben kasar ta dakatar da shi.
Yanzu dai ya ci gaba da shirye-shiryen tare da dora yakin neman zabensa.