An saki Saadi Gaddafi, dan tsohon Shugaban Kasar Libya, marigayi Muammar Gaddafi da aka tsare a gidan yarin babban birnin kasar, Tripoli.
Tun a 2014 aka tsare Saadi Gaddafi wanda shi ne kwamandan runduna ta musamman a lokacin gwamnatin mahaifinsa, wanda aka kifar da gwamnatinsa aka kuma kashe shi.
Saadi Gaddafi tsohon dan kwallo ne a gasar Serie A ta kasar Italiya, ya kuma tsere daga Libya ne bayan kifar da gwamnatin mahaifinsa.
Sakin nasa ya samo asali ne daga tattaunawar da kusoshin manyan kabilun kasar da kuma Fira Minista Abdulhamid Dbeibeh suka yi.
Wata majiyar ta ce tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar, Fathi Bashagha, na daga cikin wadanda suka sa baki a tattaunawar.
Rahotanni sun nuna cewa jim kadan bayan sakin sa daga gidan yari na Tripoli, Saadi Gaddhafi ya haye jirgi zuwa birnin Santambul na kasar Turkiya.
Gwamnatin hadakar kasar Libya ta ce tana fata sakin nasa da aka yi zai taimaka wurin kawo hadin kai tsakanin bangarorin da ba sa ga-ma-ciji da juna a kasar.