✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liberpool da Arsenal da PSG sun fara rububi a kan Kante

Kulob din Liberpool shi ne na baya-bayan nan da ya shiga sahun wadanda suke zawarcin dan kwallon tsakiya a kulob din Liecester City da ke…

Kulob din Liberpool shi ne na baya-bayan nan da ya shiga sahun wadanda suke zawarcin dan kwallon tsakiya a kulob din Liecester City da ke Ingila Ngolo Kante don ganin sun dauke shi kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Daily Stars ta ruwaito, kocin kulob din Arsenal Arsene Wenger ya nuna sha’awarsa a kan dan kwallon, sai dai farashin Fam Miliyan 22 da kulob din Leiecester ya sagala wa dan kwallon ne yake neman ya tsorata shi.
Rahotanni sun tabbatar sau biyu kenan wakilan kulob din PSG da ke Faransa suke tattaunawa da jami’an kulob din Leicester a kan yiwuwar saye Kante.
Shi ma kulob din Liberpool an ruwaito ya amince ya ajiyewa Leicester City Fam miliyan 22 don ganin ya dauke dan kwallon.
Kante, dan kimanin shekara 25 yana daga cikin ’yan kwallon da suka taimakawa kulob din Leiecester lashe kofin firimiya na Ingila a karon farko a kakar wasan da ta wuce.  Hakan ya sa kulob da dama suka shiga rububin ’yan kwallon kulob din ciki har da Kante da Jamie bardy da Riyad Mahrez da sauransu.