Kulob din Liverpool da ke Ingila ya kammala shirin sayen dan kwallon Najeriya Victor Osimhen kamar yadda kocin kulob din Jurgen Klopp ya sanar a ranar Talatar da ta wuce.
Kulob din ya ce zai yi zawarcinsa ne da zarar an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a wannan wata na Janairu.
Victor Osimhen wanda ya sanya wa kulob din Lille na Faransa hannu a watan Yunin bara, kawo yanzu ya zura kwallo 13 a raga a dukkan wasannin da ya yi wa kulob din a kakar bana.
Osimhen wanda tauraruwarsa ke haskakawa a bana, kulob da dama suna rububi a kansa da suka hada da FC Barcelona na Spain da Tottenham da Chelsea da kuma Liverpool dukkansu a Ingila da sauransu.
Osimhen yana daga cikin matasan ’yan kwallon da za su fafata a Gasar Gwarzon Matashin Dan Kwallon Afirka ta bana a ranar Talata mai zuwa a Masar.