✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lemon kwakwa da madara

  Kayan hadi: . Kwakwa . Madarar kwakwa ko madarar ruwa . Sirof ko sukari . Filebo   Yadda ake hadawa: Da farko uwargida za…

 

Kayan hadi:

. Kwakwa

. Madarar kwakwa ko madarar ruwa

. Sirof ko sukari

. Filebo

 

Yadda ake hadawa:

Da farko uwargida za ki gyara kwakwarki, ki cire bakin da ke jiki.

Sa’annan sai ki wanke ta tas ki goge. Sai ki zuba ruwa a kai, sa’annan ki tace. Sai ki dauki ruwan ki juye a cikin kofin da kike hada lemo a ciki.

Sa’annan sai ki dauko madarar kwakwa (Coconut milk ko kuma madarar ruwa) sannan sai ki zuba ruwan sukari na sirof, Sa’annan sai ki kawo filebo ki zuba akai. Sai ki bar shi ya yi sanyi.