✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Leicester City ta saye Luis Hernandez

kungiyar kwallon kafa ta Leicester City da ta lashe kofin Premier na Ingila a bana ta sayi dan wasan kwallon kafa dan kasar Spain Luis…

kungiyar kwallon kafa ta Leicester City da ta lashe kofin Premier na Ingila a bana ta sayi dan wasan kwallon kafa dan kasar Spain Luis Hernandez inda zai buga mata kwallo na tsawon shekara hudu daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa. Luis Hernandez mai shekara 27, zai koma kungiyar ne a matsayin aro idan kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Sporting Gijon da ke Spain ya kare.
Hernandez ya buga wa Sporting Gijon kwallon sau 140 tun lokacin da ya koma can a shekarar 2012.
Kuma ya fara samun horo ne a gurbin matasa na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid duk da dai bai buga wa babbar kungiyar wasa ba.