✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Laylah Ali Othman: Matashiyar da ba ta san zaman banza ba

Laylah Ali Othman ta yi karatu a kasashe daban-daban na koyon sana'a

Mai yiwuwa a yi tunanin babu abin da ’yan  shekara 19 za su iya sani game da kasuwanci; amma Laylah Ali Othman tana da wadannan shekarun ta fara saye da sayarwa na kashin kanta.

A yanzu haka kuma ita ce Manajan Darakta a kamfanin Superb L&N Interiors and Exterior Décor, masu kawata gine-gine.

Saboda burin da take da shi na ganin wasu sun amfana da basirar da Allah Ya yi mata a wannan bangaren kuma, har makaranta ta bude ta koyar da dabarun kawata gine-gine.

Tana kuma da dakunan sayar da abinci a wasu unguwanni a Abuja.

Ilimi ga marasa galihu

Burin Laylah Ali Othman na ilmantar da al’umma ba ga koyar da kawata gine-gine kawai ya tsaya ba.

Ta kafa wata gidauniya mai suna Laylah Initiative for the Boy and Girl Child Charity Foundation (LIBGC) wadda ke daukar nauyin ilimin yara marasa galihu maza da mata, musamman almajirai.

Sannan kuma ta hanyar shirinta na talabijin, “Laylah’s Way”, tana tuntuba ta kuma sauya rayuwar mutanen da ba su da karfi ta sauya musu fasalin gidajensu.

Tauraruwar tamu dai tana fitowa a shirye-shiryen talabijin wadanda suka hada da “Muryar Jama’a” mai tattauna rayuwa da al’adun Hausawa.

Tana kuma da wata mujalla mai suna L. Magazine mai duba batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da salon rayuwa.

Haka kuma Laylah Ali Othman ta wallafa littattafai biyu, Something Deep da Masked.

Kafofin sadarwa na zamani

Laylah mace ce da ta tsaya da kafafunta sannan take taimaka wa wasu. Daliban da take daukar nauyinsu suna karatu a matakai daban-daban, kama daga naziri zuwa makarantun gaba da sakandare.

Burinta na ganin ta yi zarra ne yake kara mata kaimi. Ta kan huta ne ta hanyar karatu, ko tukin mota ko kuma cin abinci.

Mutane da dama dai sun san Laylah ne ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.