A zaben Gwamna da na ’yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga Maris ne Lawan Musa Majakura mai shekara 33, ya kayar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Ahmed Mirwa Lawan da kuri’a 182 don wakiltar Mazabar Nguru II a Karamar Hukumar Nguru a Jihar Yobe.
Aminiya ta tattauna da zababben dan majalisar na Jam’iyyar PDP ta waya, inda ya yi bayani kan takaitaccen tarihi da harkokin siyasarsa da yadda ya samu nasarar da ta yi waje da Shugaban Majalisar:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
An haife ni a garin Majakura da ke Karamar Hukumar Nguru a watan Janairun 1990. Na yi karatun firamare a Majakura.
Daga nan na wuce Kwalejin Gwamnati da ke Nguru, inda na samu karamar Diploma a Nazarin Addinin Musulunci.
Daga nan na tafi Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Damaturu, inda na kammala a shekarar 2009 tare da samun takardar Babbar Diploma (HND) a fannin kasuwanci da Gudanarwa a 2020.
To amma ban samu damar yi wa kasa hidima ba (NYSC) saboda shekaruna sun zarta shi ya sa na samu takardar shaidar yawaitar shekaru kamar yadda tsarin hakan ya nuna.
Daga nan ne na tsunduma cikin harkar sayar da kifi da sauran abubuwan da za su ba ni wani abu don ci gaba da bukata ta.
A halin yanzu ina da mata daya da ’ya’ya hudu.
An zabe ka dan Majalisar Dokokin Jiha, ko ka taba tsayawa takarar wani mukami?
Eh, lallai na taba tsayawa takarar kansila a 2021 lokacin ina Jam’iyyar APC kafin in koma PDP, amma ban samu ba.
Mutanenmu musamman matasa, sun ce in yi takara, domin suna ganin zan iya yin abin da ya fi haka, amma Allah bai Sa na dace ba a wancan lokaci, daga bisani muka yi addu’ar Allah Ya ba mu matsayi mafi alheri da za mu taimaki al’umma.
Alhamdulillah Allah kuwa Ya karbi addu’armu da na manyanmu ga shi yanzu na zama dan majalisar dokoki.
Kamar yadda muka samu labari a baya an ce akwai lokacin da wasu jami’an tsaro suka kama ka, kuma suka tsare har sau uku saboda sukar shugaban majalisar da wasu ’yan siyasa a Facebook. Mece ce gaskiyar hakan?
A gaskiya an kama ni sau biyu. Daya daga cikinsu ya fito daga wani dan siyasa a Jam’iyyar APC kafin in bar jam’iyyar, bayan na yi masa suka a Facebook, sai ’yan sanda su kama ni suka tsare ni na tsawon kwana biyar.
Na biyu shi ne na Shugaban Majalisar wanda na yi suka a kan rashin wakilci nagari da yake mana mu al’ummar Mazabar Nguru 11.
An kama ni aka tsare na tsawon awa 48 wato a bara a cikin watan Ramadan wato kamar yanzu.
Kuma abin da ke jawo min irin wannan kamu bai wuce duk lokacin da na ji cewa gwamnatin jiha ta amince da aikin mazabu ga ’yan majalisar jiha, nakan tabbatar da inda aka kashe namu kudaden, idan yana da wani tasiri a cikin al’ummarmu, inda nakan bi diddiginsu don ganin an yi aikin.
Don haka matukar na ga ya gaza yin abin da ya dace nakan soke shi a duk lokacin da na gano cewa muna da matsalar da zai iya magancewa amma ya kasa yin haka, kuma nakan yi suka ce ta gaskiya babu son zuciya a ciki hakan ke haifar min da kamu da tsarewa.
Me ya jawo hankalin ka, ka tsaya takara da Shugaban Majalisar wanda ya shafe shekara 20 a majalisar har ya kai matsayin da yake kai a yanzu?
Hakikanin gaskiya abubuwa da yawa sun yi tasiri kan tsayawa takararta.
Abu na farko, fannin ilimi, muna da komawa baya a kauyenmu na Majakura kuma mukan ga yadda abubuwa suke faruwa kowace rana inda ajujuwanmu sun lalace ga kuma karancin ayyukan yi ga matasanmu masu yawa haka nan a bangaren lafiya nan ma haka lamarin yake don haka na gane cewa rashin wakilci mai kyau ya haddasa mana shiga cikin wannan yanayi.
Don haka don magance wadannan kalubale ne, ya sa mutanenmu suka ce in tsaya takara watakila suna tunanin zan yi abubuwa daban da za su taimaka musu.
Ka ce mutanenka suka ce ka fito takara, ko sun ba ka wani tallafi don yakin neman zabe?
Eh, sun saya min fom din takara. Sun kuma ba da gudunmawar kudi don yakin neman zabe kuma ba su tuntube ni ba ko ina da sha’awa ko a’a.
Sai kawai suka sayi fom suka ce suna so in tsaya takara, ni kuma ban tambaye su nawa suka sayi fom din ba, nan take na cika na mayar musu da shi.
Ka san cewa lokacin da kake neman kujera a kowace jam’iyya akwai zaben fid-da gwani, amma na yi nasara ba tare da hamayya ba a jam’iyyata ta PDP.
Mutanen kauyena wadanda galibi manoma ne da masu sayar da kifi, su ma sun tara min kudi don yakin neman zabe cikinsu akwai wadanda sukan kira ni ta waya suna yi min fatar samun nasara, wasu kuma su tura Naira dubu 20 zuwa dubu 50 a asusun bankina, duk don suna ganin zan iya yin abubuwan da suka dace matukar na kai ga nasara.
A lokacin yakin neman zabenmu, an yi ta tursasa wa mutane saboda bambancin jam’iyya, amma alhamdulillahi duk da kalubalen da aka fuskanta mun samu nasarar cin zabe, amma dai ba abu ne mai sauki ba kayar da Shugaban Majalisar Dokoki ta Jiha.
Ko Shugaban Majalisar ya tuntube ka kafin zabe a kan ka janye masa?
Maganar gaskiya bai tuntube ni don in janye takararta shi da kansa ba. Amma wani jami’in gwamnati da wasu da nake tunanin wakilansa ne sun zo min sau biyu suna cewa in janye.
Sun yi alkawarin ba ni Naira miliyan 18, amma na ki, daga baya suka dawo suka yi min tayin Naira miliyan100, amma na ki.
Na ce da su mutanen kauyenmu ne suka sayo min fom don tsayawa takara saboda sun yi imanin cewa zan yi abubuwan da suka kamata in na samu nasara.
Don haka ban ga dalilin da zai sa in janye daga takara ba. Da na ga sun matsa sai na ce su je su hadu da mutanena idan da gaske suna son in janye takarata ga duk wanda ya aiko su gare ni.
Daga bisani na gaya wa jama’ata abin da muka tattauna amma duk mun yarda cewa ba zan janye ba, sai muka ci gaba da yakin neman zabe ba tare da sake saurararsu ba.
Wane abu za ka sa gaba in ka shiga majalisa domin al’ummar mazabarka?
A koyaushe muna yin abubuwa daban misali, kamar yadda nake magana da ku, ina da ’yan mata sama da 25 da maza 30 da suka samu karatun sakandare ta hanyar tallafi da horarwa.
Shugaban Majalisar ba zai iya gaya muku adadin mutanen da ya taimaka wajen cimma wannan buri ba kasancewar ban yi tsammani yana da abin fada ba kan haka.
Dangane da kyakkyawan wakilci, zan ba da fiffiko ga ilimi ta hanyar gyara azuzuwanmu tare da tabbatar da mun dauki kwararrun malamai da samar da kayan koyo da koyarwa.
Na biyu, cibiyoyin kula da kiwon lafiyarmu suna bukatar kulawa sosai ta hanyar samar da magunguna da ma’aikatan lafiya kwararru lura da cewa muna da al’ummomi masu yawa.
Har ila yau zan kokarta wajen samar da ruwa da kuma sauran kayan more rayuwa.
Haka nan zan matsa ta wajen rokon gwamnati ta yi wa mutanenmu abubuwan da suka dace na ci gaban su, kuma zan yi duk mai yiwuwa wajen gabatar da kudiri don tabbatar da cewa an sake gina hanyoyinmu da suka lalace a mazabata in Allah Ya so.
Akwai mutane da dama da suka kammala karatu amma ba su da aikin yi kuma makarantunmu na bukatarsu, don haka zan tabbatar da cewa gwamnati ta dauki irin wadannan mutanen aiki, walau aiki na wucin-gadi ko na dindindin.
Zan tabbatar cewa ina tare da mutanena a kowane karshen mako don jin matsalolinsu da abin da zan iya yi don magance su.
Idan ba zan iya magance matsalolin ba zan kai su ga bangarorin da suka dace don daukar mataki a kai.
Gwamna Buni ko Shugaban Majalisar akwai wanda ya kira ka don taya ka murnar lashe zabe?
Gaskiya babu daya daga cikinsu da ya kira ni ya taya ni murna, amma na samu sakonnin taya murna daga ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa da ’yan jarida da kuma kungiyoyin farar hula.
Sakonnin wadannan mutane sun karfafa ni, don haka ban damu da sakon Shugaban Majalisar ba.
Sakamakon zaben ya nuna Jam’iyyar APC na da kujerun ’yan majalisa 22 yayin da jam’iyyarku ta PDP ke da biyu, ku ’yan tsiraru ne da hakan na iya shafar aikinku, ko akwai yiwuwar ku sauya sheka zuwa APC?
A gaskiya ba zan ce komai ba domin Allah ne kadai Ya san abin da zai faru yau ko gobe, Na san cewa Gwamna Buni mutum ne mai tawali’u mai basirar shugabanci, don haka bisa fahimtata da shi ba zai bari bambancin jam’iyya ya yi tasiri ga ci gaban Nguru ko Jihar Yobe ba.
Abin da zan iya cewa shi ne, zan yi duk mai yiwuwa don ganin na isar da sako da matsalolin al’ummar mazabata wadanda aka bari a baya ga gwamnatin jiha da bin duk hanyoyin da suka dace, tare da fatar magance su.
Insha Allahu ba zan taba bata musu rai ba dangane da bukatunsu.