A ci gaba da shari’ar da ake fafatawa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, lauyan wanda ake kara sun bukaci a dawo musu da shaidar da aka gabatar na farko don su sake yi masa wasu tambayoyi.
Lauyoyin sun bukaci hakan ne yayin zaman kotun ta Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu ranar Alhamis.
- ’Yan bindiga sun kashe Dagaci da wasu mutum 5 a Katsina
- Tsohuwar sarauniyar kyau ta Amurka ta kashe kanta bayan fadowa daga bene mai hawa 30
Ana dai zargin malamin ne da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tayar da hankali.
A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyoyin wanda ake kara, karkashin jagorancin Barista Ambali Obomeileh Muhammad (SAN), sun roki kotun da ta dawo musu da shaida na farko da masu gabatar da kara suka kawo gabanta don su sake yi masa wasu tambayoyin.
“Duba da girman laifin da ake zargin wanda muke karewa, muke ganin akwai bukatar a sake ba mu dama don mu sake yi wa wannan shaida tambayoyi kafin mu shiga kariya a zama na gaba,” inji lauyoyin.
Sai dai bangaren masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Suraj Sa’ida sun yi suka inda suka ce yin hakan bata lokaci ne ga tsarin tafiyar da shari’ar don haka suka roki kotun da ta yi watsi da rokon lauyoyin wanda ake kara.
“Duba da cewa an ba wanda ake kara isasshen lokaci na makonni hudu da su yi duk abin da ya kamata kafin zuwan wannan rana ta yau da aka ajiye a matsayin ranar da za su fara kariya amma sai suka zo da wannan batu. Mu a ganinmu, hakan kawo tsaiko ne ga wannan sharia.
“Baya ga haka wannan shaidar da ake magana a kansa yana can Jamhuriyar Nijar yana karatu haka kuma Allah (SWT) ya hana wahalar da shaida. Don haka muka yi suka akan wannan roko tare da neman kotun ta yi watsi da wannan roko nasu,” inji lauyoyin gwamnati.
Da yake yanke hukunci a kan lamarin, alkalin kotun, Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ya amince da bukatar lauyoyin wanda ake kara inda ya umarci bangaren masu gabatar da kara da su sake gabatar da shaidarsu na farko don sake amsa tambayoyin lauyoyin wanda ake kara.
Dagan an sai ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairun 2022.