Lauyan da ke kare Abduljabbar Kabara, wato Barista Dalhatu Shehu Usman, ya zargi Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman da hadin baki da Gwamnatin Jihar a shariar da ake yi wa wanda yake karewa.
Lauyan ya bayyana haka ne jim kadan da fitowa daga zaman shari’ar a ranar Laraba, inda ya nemi a mayar da shari’ar zuwa wata kotun a Abuja sakamakon tafiya hutu da kotun za ta yi.
- Sabuwar shekarar Musulunci: Ganduje ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutu a Kano
- Rundunar Sojojin Sama za ta fara kera jirage a Najeriya
Tun da farko, lauyan ya garzaya gaban kotun ne yana neman ta dakatar da kotun kasa ta Shariar Musulunco daga ci gaba da sauraron tuhumar da ake yi wa Abduljabbar Kabara bayan da Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da shi gabanta bisa zargonsa da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) da kuma tayar da hankulan jamaa.
A cewar Barista Dalhatu, “Kafin zaman kotun a yau, mun sami labarin zuwan Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano ofishin Alkalin Kotun inda suka dauki tsawon lokaci suna tatraunawa a tsakaninsu.
“Hakan ya sa muke shakkun cewa wannan kotun ba za ta yi mana adalci ba, don haka muke neman canjin kotu zuwa Abuja,” inji lauyan.
Shi ma lauyan Gwamnati, Barista Muhammad Dahuru ya bayyana cewa, “Lauyan Abduljabbar Kabara ya zo da tsaiko a wannan shari’a domin ya sake shigar da kara iri daya a gaban kotu mai lamba takwas da ke Abuja wanda kuma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba domin kotun tarayya guda daya ce.”
Sai dai kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 23 ga watan Satumban 2022.