✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lambar NIN: Ba za a rufe layukan waya ba

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce ba za ta rufe duk layukan wayan ’yan Najeriya da ba su hada su da Lambar Shaidar Zama…

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce ba za ta rufe duk layukan wayan ’yan Najeriya da ba su hada su da Lambar Shaidar Zama Dan Kasa ta NIN ba.

Kakakin NCC Ikechukwu Adinde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa domin karin bayani game da fargabar da ’yan Najeriya ke ciki game da rufe layukan marasa rajista da lambar NIN.

“Bincikenmu ya nuna mutun daya na da layukan waya hudu zuwa biyar. Shi ya sa muke so mu hade lambobin waya, ko da sun kai bakwai, da lambar NIN guda daya a rumbun adana bayanai na Gwamnatin Tarayya”, inji Mista jami’in.

Adinde ya ce ’yan Najeriya da yawa sun riga sun yi wa layukan wayansu rajista da lambar NIN don haka babu abin damuwa.

Ya kara da cewa idan mutum miliyan 43 suka na da lambar NIN a Najeriya, abin nufin shi ne yi wa layuka kusan miliyan 172 rajistar NIN ke nan.

Ya jaddada cewa tsarin hade layukan waya da lambar zai amfani ’yan Najeriya ta hanyoyi da dama.

“Baya ga tabbatar da tsaro, zai kuma taimaka wajen tsara kasafin kudi, da shirye-shiryen gwamnati na tallafi da sauransu”, kamar yadda ya yi bayani.

A baya Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya ba da tabbacin cewa za a rika waiwayan tsarin da aka bullo da shi domin kawar da duk matsalar da aka samu.