✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lallai ne a dauki matakin dawo da ’yan matan Chibok

Daga dukkan alamu dai al’amarin ’yan matan Chibok na neman ya gagari kundila, domin kuwa an shiga wata na hudu ke nan cur da ’yan…

Daga dukkan alamu dai al’amarin ’yan matan Chibok na neman ya gagari kundila, domin kuwa an shiga wata na hudu ke nan cur da ’yan Boko Haram suka sace su, amma an kasa ceto su. Dalili ke nan mutane ke ta nuna tausayi da alhini ga al’amarin. A wannan makon, marubuciya mai tsokaci kan al’amuran al’umma, Malama A’isha Usman Liman (09093467171), ta dauki alkalaminta ta rubuta wannan tsokacin:
Haba! Haba!! Haba, shuwagabanninmu!!! Wannan wane irin rashin kulawa ne, wane irin rashin tausayi ne; wane irin rashin katabus da kuzari da kazar-kazar ne haka, a ce yara sun kwashe fiye da kwanaki dari ba a gidan iyayensu ba, suna a hannun ’yan ta’adda amma a ce hukuma ta rasa dubarar da za ta yi ta karbo su, ta rasa kokarin da za ta yi ta kwato su, ta rasa hikimar da za ta yi ta ceto su? Wannan wace irin kasa ce muke cikinta, wadanne irin shuwagabanni ne muke da su?
To, gaskiya wannan al’amari yana da ban tsoro da ban mamaki da ban kunya, a ce shuwagabannin kasa kamar Najeriya sun kasa tsare lafiyar talakawansu.
Ya ku shuwagabannin kasarmu Najeriya, da duk ’yan kasa, kowa ya kudurta a ransa cewa wadannan ’yan matan Chibok da aka sace a cikinsu akwai ’yarsa ko kanwarsa ko matarsa, kai koma dai wata yarinya da ya shaku da ita a cikinsu;   in shi ne ya zai ji da kewa da tausayinta? Mu tuna fa, yaran nan a jeji suke, duka rayuwarsu yanzu ta koma a jeji kamar dabbobi kuma a kan tilas ba don sun so ba. Mu kudurta a ranmu kuma mu auna ya rayuwar zama a jeji take ga wanda aka sace, aka tilasta masa yin ta?
Shin suna samun abinci a wadace akalla sau uku a yini? Ba a maganar ma mai gina jiki ko mai dadi. Shin suna samun ruwan sha isasshe? Ba a ma maganar tsarkakakke, mai tsafta. Shin a ina suke kwana, cikin tanti ne ko cikin bukka ko a sararin Subuhana ne? Ba za mu yi tunanin suna kan tabarma ba, balle a kan katifa da filo.
Shin idan ciwo ya bijiro wa daya daga cikinsu, ko wasunsu, ya suke ji, me ake ba su su samu sauki? In ma mun kudurta cewa akwai asibiti ko dakin magani, shin mai ba da maganin likita kwararre ne, ko jeka-na-yi-ka ne? Shin ana auna cututtukansu, ko dai magani kawai ake aunawa a ba su su sha? Ba za mu yi tunanin cewa suna samun waraka ba balle mu yi tunanin suna nan cikin koshin lafiya.
Shin, tun da ’yan mata ne, yaya suke yi idan al’ada ta zo masu, suna samun yadda za su tsabtace kansu da wani tsumma ko auduga? Shin ko akwai mai tunanin wadannan ’yan ta’adda za su iya wadata su da auduga da kanfe ko duros?
Shin suturarsu (daya kacal da suke sanye da ita lokacin da aka sace su), ya take ciki a halin yanzu? Ko za mu iya tunani da cewa duk an yi musu sababbin dinkuna? Su fiye da dari biyu? To, in ba a yi ba fa, haka suke ta fama da wadannan suturar kala daya, fiye da kwana dari? Shin suna wanka da wanki, ina suke samun sabulu? Shin suna kitso ko gyara gashinsu, to ina suke samun abin taje kai? Shin suna yanke kumba, to ina suke samun reza ko abin cire kumbar?
Duk wadannan tunani da tambayoyin da muka ambata da ma wadanda ba mu ambata ba, suna nan ba iyaka. Sai dai mu abin nufin mu a nan shi ne, kowa ya yi tunani a ransa cewa idan akwai nasa a cikinsu; ina zai samu amsoshin wadannan tambayoyin kuma ya zai yi ya ceto wadannan ’yan mata, ya dawo da su cikin gatansu (iyayensu)?
Wannan fa duk a gefen ’yan matan ke nan, to a gefen iyayensu, wane hali suke ciki? Duk wani mai rai da hankali ya san cewa hali na jira ko dako ko tsammani a kan abin bukata radadi ne da shi kuma masana harkar lafiya sun shaida mana cewa a irin wannan halin, zuciya kan shiga yanayi na tafasa ko azazzala don tsimaye ko kwadayin ganin ta samu abin da take dako ko jira. To wannan halin shi ne zukatan iyayen ’yan matan Chibok suke ciki ba dare ba rana fiye da kwanaki dari.
Yau inda yaran nan kashe su aka yi a cikin makarantarsu, iyayen suka ga gawarwakinsu, suka binne su, to da yanzu sun yi kuka da alhini har sun hakura sun bar wa Allah, tun da sun san sun rasa su har abada. Amma hali irin wannan na zullumi da tausayi da rashin madogara ya fi komi bakin ciki da musgunawa, tare da illata zukata da rayuwa ga baki daya.
To, yanzu mene ne magani ko mafita ga wannan hali da ’yan matan Chibok da iyaye da abokan arziki suke ciki? Amsa kam sai dai ga shuwagabanni da hukuma, domin su kadai suke da alhakin samo hanyar da za a bi a kubuta daga wannan hali da ake ciki.  Hukuma alhakin tsaron kasa yake hannunta, hukuma ke da ikon zartarwa da kaddamarwa, ita ke da hanyoyi da dabara da hikimar aiwatarwa, ita ke da karfi da kuzarin wanzarwa.
To, yanzu ita hukumar kasarmu Najeriya ba ta da duk wasu hanyoyi ne da har yaran nan za su kwashe kwananki day-daya har fiya da dari ba ta dawo da su hannun iyayensu ba? Idan ko tana da su to me ya hana? To mu dai nuna rokon ta, ko ma mene ne ya sa take tafiyar hawainiya a cikin wannan al’amari, ta yi hakuri ta bar shi, ta dubi wannan matsalar cikin kulawar gaggawa da hanzari, ta yi tunani da halin da yaran nan da iyayensu suke ciki, ta ceto ’yan matan Chibok haka nan. Domin mu dai ba mu tunani da cewa hukumar kasarmu ta gaza, saboda kasarmu ta shahara wurin kai dauki da agaji ga wasu kasashen da suke da matsalar yaki ko tawaye, balle irin wannan ta ’yan ta’adda irin ’yan Boko Haram, sai dai mu yi tunani ko dai akwai wani boyayyan dalili ko manufa da suka sa hukuma ba ta dauki abin cikin halin hanzari ba, wanda mu ba mu sani ba!
Mu dai rokonmu koma mene ne, hukuma da shuwagabanni su yi tunani a ransu, duk wanda ke cikin tsanani fatan shi a gaggauta kai masa dauki da agaji. Gaskiya yaran nan ya kamata mu nuna masu kauna da tausayawa, kuma mu nuna masu kasarsu na da mahimmanci a gare su. Kar mu bari su fara tunanin tsana da kyamar kasarsu da shuwagabanninta.
Wadannan yara fa su ne manyan gobe kuma iyayen manyan gobe. Me muke tunani zai faru idan rayuwarsu ta dore cikin wannan hali? Me za su zama kuma me za su haifa? ’Yan ta’adda kuma uwayen ’yan ta’adda?
Lalle kam idan muka yi sakaci yaran nan suka fara haihuwa da wadannan mutane, to kasarmu ba ta da makoma a rayuwa. Ku duba halin da muke ciki da su a yanzu, balle a ce sun juya wa wadannan ’yan mata ra’ayi, sun bi su har sun haihu da su; to ya ke nan kasar zata zama?
To, lallai hukuma da shuwagabanni da ’yan kasa mu sani zaune ba ta kare mana ba. Kau da kai da sakaci da ko-in-kula da ba-ta-shafe-ni ba, da ai-ba ’yan-yankina-ba-ne da ai-ba-garina-ne-ba da ai-ba ’ya’yana-ba-ne, duk wannan ba namu ba ne.
Wallahi ya kamata kowa ya yi tunani daga gefensa, ya ba da tasa gudunmawar yadda za a yi a ga an ceto wadannan ’yan mata cikin hanzari tun kafin a haifa mana bala’in da zai iya mamaye mana kasa da ma Afirika baki daya.
Ya Allah Ka sa hukuma da shuwagabanni da ’yan kasa su ankara kuma su gane masifar da ’yan matan Chibok da iyayensu suke ciki kuma mu gane da masifar da sace su zai iya jawo mana. Amin.