✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lalata da dalibai: Poly Bauchi ta kori malamai daga aiki

Dubun lakcarorin ta cika bayan dalibai mata sun kai kara ga mahukunta kwalejin.

Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Bauchi ta kori wasu malamanta biyu saboda kama su da laifin yin lalata da dalibai mata.

Hukumar gudanarwar kwalejin ta yanke hukuncin korar malaman da suka yi lalata da dalabai ne a zaman da ta gudanar a ranar Asabar.

Shugaban Kwalejin, Sanusi Gumau, ya ce “Dokar kwalejin ta tanadi  cewa a duk lokacin da aka samu babban zargi irin wannan, to mataki na farko da ake dauka shi ne yin bincike.

Ya bayyana haka ne a yayain ganawa da manema labarai.

Wasu masu kusanci da kwalejin sun ce an kama malaman da laifin yin lalata da dalibai ne bayan kwamitin binciken da kwalejin ya kafa ya kammala aikinsa ya gabatar da rahoto.

Kwalejin ya kafa kwamitin binciken ne bayan wasu dalibai mata da abin ya shafa sun gabatar da korafi ga mahukunta kwalejin.

%d bloggers like this: