Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Bauchi ta kori wasu malamanta biyu saboda kama su da laifin yin lalata da dalibai mata.
Hukumar gudanarwar kwalejin ta yanke hukuncin korar malaman da suka yi lalata da dalabai ne a zaman da ta gudanar a ranar Asabar.
- Facebook ya shiga tsaka mai wuya kan yada labaran karya
- An kama mai shayarwa ta kai miyagun kwayoyi ofishin NDLEA
Shugaban Kwalejin, Sanusi Gumau, ya ce “Dokar kwalejin ta tanadi cewa a duk lokacin da aka samu babban zargi irin wannan, to mataki na farko da ake dauka shi ne yin bincike.”
Ya bayyana haka ne a yayain ganawa da manema labarai.
Wasu masu kusanci da kwalejin sun ce an kama malaman da laifin yin lalata da dalibai ne bayan kwamitin binciken da kwalejin ya kafa ya kammala aikinsa ya gabatar da rahoto.
Kwalejin ya kafa kwamitin binciken ne bayan wasu dalibai mata da abin ya shafa sun gabatar da korafi ga mahukunta kwalejin.