Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman Ya tsare mu daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu.
Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ManzonSa ne.
Bayan haka ya bayin Allah masu girma! Ku ji tsoron Allah Madaukaki, kuma kada ku yarda ku mutu face kuna Musulmi.
Kuma ku kiyayi aikata laifuffukan da za su jawo wa al’umma masifu.
Allah Madaukaki Ya ce: “Ku ji tsoron (aikata) fitinar da (idan ta zo) ba za ta cutar da wadanda suka jawo ta su kadai ba…” (Suratul Anfal:25)
Daga cikin wadannan laifuffuka Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambaci guda biyar a wani Hadisi da Dabarani ya ruwaito daga Abdullahi dan Abbas cewa: “Abubuwa biyar suna jawo (masifu) biyar:
1. “Mutane ba za su warware alkawari ba, sai an rinjayar da abokan gabansu a kansu.” Ma’ana cika alkawari wajibi ne a kan Musulmi. Alkawari na tsakaninka da Allah da kuma tsakaninka da mutane.
Da yawa mutane sukan yi alkawarin taimakon addinin Allah (ko taimakon bayin Allah) amma ba su cikawa.
Haka alkawari a kan aiki ko wata hidima, kadan ne suke cikawa.
Har ta kai ga Musulmi ba su iya gudanar da komai a kan lokaci, sai sun saba alkawari.
Allah Madaukaki Ya ce: “Ku cika alkawari! Lallai ne alkawari abin tambaya ne.” (Suratul Isra’i :34)
2. “Ba za su yi hukunci da wanin Littafin Allah ba, face talauci ya yadu a cikinsu.” Ma’ana rashin hukunci da Littafin Allah shi ne tushen yaduwar talauci a cikin al’umma.
Yau Musulmi nawa ne suke hukunci da Littafin Allah a kansu. Musulmi nawa suke tilasta wa kansu yin sutura irin yadda shari’a ta ce a yi, kamar mutum bar gemunsa saboda bin shari’ar Allah.
Mace nawa take sakin hijabinta kamar yadda shari’a ta ce. Abin da wadansu mazaje suka dauka a yau shi ne wayewar kai, shi ne su saki wandunansu har kasa suna take shi, mace kuma ta bayyana gashinta a waje.
Sun dauka alama ce ta kauyanci a gan ka ka dage wando kamar yadda Allah Yake so. Wal’iyazu-Billah! Shari’ar da za ka yi wa kanka ma ka kasa yi, to yaushe za ka yarda da shari’ar da wani zai zartar maka.
Kamar yanke hannun barawo ko jefe mazinaci da sauransu?
3. “Alfasha ba za ta bayyana a cikinsu ba, face mace-mace sun yadu a cikinsu.”
Ma’ana idan ana zinace-zinace a bayyane, har ta kai ga an samar da gidaje sanannu da mata fitattu, ta yadda za ta kai har an san wadannan gidaje na zinace-zinace ne, wadannan mata sana’arsu ita ce zina, ita suke yi su ci abinci su yi sutura.
Idan an samu haka a cikin al’umma, Allah zai saukar da cututtukan da za su yi ta kashe mutane.
Cutar kanjamau ta isa misali, kowa ya san da ita. Mutane da yawa sun bar zina saboda tsoron kamuwa da ita, ba saboda tsoron Allah ba.
4. “Mutane ba za su tauye mudu ba, face an hana su albarkar amfanin gona, kuma an saukar musu da fari.”
Ma’ana tauye mudu shi ne sanadin rashin samun amfanin gona mai yawa mai albarka. Kuma shi ne yake kawo fari.
Yau mutum nawa suke cika awo? Wadansu na lotsa kwanon awonsu, wadansu na tsoma fatun buhuna a ruwan zafi domin su motse kafin su dura hatsi da sauransu.
Alhali Allah Madaukaki Ya ce: “Bone (azaba) ya tabbata ga masu tauyewa.
Wadanda idan suka auna daga mutane suna cikawa (mudu). Amma idan su za su aunar da mudu ko da sikeli sai su tauye.” (Suratul Mudaffifin: 1-3)
5.”Mutane ba za su hana Zakka ba, face an tsare (hana) musu ruwan sama.”
Yau mutane kadan ne suke fitar da Zakka, wadansu ma suna sayen kadarori su ajiye su ki fitar da Zakka.
Wadansu za su gina manyan gidaje su bayar da su haya, kuma su dauka babu Zakka a kan gidajen. Allah Madaukaki Ya ce: “Bone (azaba) ya tabbata ga mushrikai. (Su ne) Wadanda ba su fitar da Zakka.” (Suratu Fussilat: 6-7).
Daga cikin abubuwan da suke jawo wa al’umma masifu akwai rashin yin wa’azi.
Yau kadan ne daga cikin jama’a wadanda suke yin wa’azi. Wani ko matarsa da ’ya’yansa da abokansa ba ya iya yi musu nasiha a kan wani abu da suke yi marar kyau.
Allah Madaukaki Ya ce: “An la’anci wadanda suka kafirta daga ’ya’yan Isra’ila a kan harshen (Annabi) Dawuda da (Annabi) Isa dan Maryama, sakamakon sabon Allah da keta haddi da suke yi.
Kuma saboda sun kasance ba su hana junansu aikata mummunan aiki.” (Suratul Ma’idah: 78-79).
Annabi (SAW) ya ce: “Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, lallai ku yi umurni da kyakkyawan aiki, kuma lallai ku yi hani ga mummunan aiki, kuma lallai ku kama hannayen wawayenku, ku dora su a kan gaskiya.
Ko kuma Allah Ya doka zukatan sashinku a kan sashi (ku yi ta fada da sabani).
Sa’annan Ya la’ance ku kamar yadda Ya la’ance su (wadanda suke gabaninku).” Ma’ana idan kun zauna ba ku yi wa juna wa’azi kowa yana yin abin da ya ga dama, kun bar samari da ’yan mata babu tarbiyya, babu ilimin addini, babu kula.
Su suke jagorantar kawunansu su suke zartar da al’amuransu yadda suke so. Allah zai sanya muku kin juna. Allahu Akbar! Wannan shi ne zahirin abin da yake faruwa a kasashen Larabawa da sauran kasashen Musulmi.
Babu wani dattijon da zai ce su je su yi, kuma babu wanda ya isa ya hana su a lokacin da suke yi.
A wani Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Allah Madaukaki Ya ce: “Ku yi umarni da kyakkyawan aiki, ku yi hani daga mummunan aiki, tun kafin ku zo kuna kiraNa ba zan amsa muku ba.
Ku nemi taimakoNa ba zan taimaka muku ba. Ku roke Ni ba zan amsa muku ba.”
Kuma wajibi ne a duk inda Musulmi suke, su tanadi abubuwa shida kamar yadda gwamnati ke tanadar wasu abubuwa bakwai:
Wato makarantar boko da asibiti da ofishin ’yan sanda da kotu da ruwa da lantarki da filin wasa, a kowane gari.
To wajibi ne su Musulmi su tanadi: Makarantar Islamiyya, inda za su yi ta koyon karatun addini, su da matansu da ’ya’yansu da masallaci wurin da za su rika yin Sallah.
Saboda shari’a ta wajabta wa Musulmi maza su rika haduwa suna yin Sallah tare da jama’a da kuma Sallar Juma’a.
Na uku malamai: Dole ne duk inda Musulmi suke su zauna da malamai, wadanda za su koya musu addini.Domin addini ba a yin sa da jahilci ko da ka.
Masallatai da yawa za ka je ka tarar an yi musu kyakkyawan gini, amma abin takaici jama’ar wurin sun kasa rike wani kwakkwaran malami su dauki nauyinsa ya zauna yana karantar da su, bayan sun dawo daga harkokinsu.
Amma kuma sai ka tarar ba za su iya zama babu likita a asibiti ba. Sun san illar ciwo amma ba su san illar yin addini cikin jahilci ba. Sai kungiyar da’awa, wato masu fita wa’azi.
Allah (SWT) Ya ce: “Lallai ne a cikinku a samu wadansu al’umma da za su yi kira zuwa ga alheri, su yi umarni da kyakkyawan aiki, su yi hani daga mummunan aiki.
Kuma wadannan su ne masu babban rabo.” (Suratu Ali Imrana: 104).
Na biyar sai makabarta. Wato wurin binne mutanen da suka rasu, sai kuma na shida filin Sallar Idi.
Shi ma ya kamata a ce Musulmi suna da shi a kowane babban gari. Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmi kuma Ya kaskantar da kafirci da kafirai, amin!
Muna rokon Allah Madaukaki Ya ba mu zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.
Duk wani mai nufin Musulunci da Musulmi da wani sharri, Allah Ka mayar masa da sharrinsa a kansa, amin!