✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lai Mohammed ya ziyarci filin wasan Madrid

Ministan Watsa Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido Alhaji Lai Mohammed a makon jiya ne ya kai ziyara ga kulob din Real Madrid na Sifen…

Ministan Watsa Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido Alhaji Lai Mohammed a makon jiya ne ya kai ziyara ga kulob din Real Madrid na Sifen inda ya shiga filin wasansu mai suna Santiago Bernabeu don kashe kwarkwatar idanu.

Wannan ziyara ta sa wasu ke ganin Ministan yana daga cikin magoya bayan kulob din Real Madrid.

Lai Mohammed ya kai ziyarar aiki kasar Sifen ce inda ya yi amfani da damar wajen kai wa kulob din Real Madrid ziyara.

Ministan wanda yake tare da masu rufa masa baya tuni ya koma gidan bayan kammala ziyarar.

Idan za a tuna, a bara ma Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya ziyarci kulob din Real Madrid a Sifen inda ya gana da mahukunta kulob din da kuma wasu daga cikin shahararrun ’yan kwallo ciki har da Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos da sauransu.

Gwamnan Ribas a yayin ziyarar ya kulla yarjejeniya ne da kulob din Madrid, inda ake sa ran kulob din zai bude Cibiyar Horar da Matasa kwallo a Jihar Ribas nan ba da dadewa ba.