Kwamatin Majalisar Dattawa mai kula da Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu ta Kasa, ya tuhumi Ministan ma’aikatar, Lai Mohammed da gaza karasa ayyuka a ma’aikatar.
Kwamantin ya kalubalanci Lai Mohammed kan gazawarsa ya karasa ayyukan da ke cikin kasafin ma’aikatarsa na bara a lokacin da ya je kare kasafin ma’aikatar na 2021.
- A tarihin Najeriya babu shugaban da ya fi Buhari yaki da talauci – Lai Mohammed
- Zulum ya fi ni kwazo ta kowace fuska —Kashim Shettima
- Kungiyar shirya fina-finai ta dakatar da Rahama Sadau
Ayyukan da majalisar ta ce ya gaza a kai sun hada da na gidan talabijin ta kasa da ke Gashua, Jihar Yobe, wanda aka kashe wa miliyan N250.
Kwamatin ya dasa ayar tambaya kan rashin gama aikin, ya kuma ce akwai tambayoyi da ministan zai amsa kan yadda ake gudanar da ayyukan ma’aikatar.