✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lafiyata kalau kuma Hamisu Breaker bai bani ko kwabo ba —Kamaye

Ni babu abin da aya same ni kuma Breaker bai bani ko kwabo ba.

Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye, ya karyata labarin da ake yadawa na cewa bashi da lafiya kuma Hamisu Breaker da Ahmed Lawan sun bashi kyautar kudi don ya nemi magani.

Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye a cikin shirin wasan kwaikwayon nan mai dogon zango wato Dadin Kowa, ya karyata labarin da ake yadawa na cewa yana fama da matsananciyar jinya.

Wani rahoto na cewa a sakamakon rashin lafiyar ce ta sa fitaccen mawakin nan Hamisu Breaker ya ba shi kyautar Naira Miliyan biyu.

Kamaye da Adama da Kawunta a yayin daukar shirin Dadinkowa

Haka shi ma Ahmed Lawan, a cewar rahoton, ya ba shi Naira dubu dari biyu don ya nemi Magani.

A hirar da Aminiya ta yi da shi bayan ta ga bidiyon rahoton, Kamaye ya ce lafiyarsa kalau.

“A ranar Alhamis na dawo daga Jamhuriyyar Nijar cikin koshin, kwanana shida a can.”

Sannan ya kara da cewa, “Ni ban san ma an yi ba, sai bayan da wata daga Saudiyya ta turo min bidiyon da aka saka a intanet. Ni babu abin da ya same ni, kuma Breaker bai bani ko kwabo ba.”

Dan Azumi Baba ya yi Allah wadai da wannan labarin karya, ya kuma ce, ya sa a nemo mishi wanda ya kirkiri wannan karyar.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kirkirar mutuwa ko rashin lafiya a kakabawa jaruman finafinai wanda daga baya a gano ba haka abin ya ke ba.