✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lafiyar mutumin da ya shekara 67 bai yi wanka ba ta ba likitoci mamaki

Rabon mutumin mai shekara 87 da wanka, tun yana shekara 20 a duniya.

Wani tsoho dan kasar Iran mai shekara 87 da yake rayuwa a kan tituna, kuma ya shafe kusan shekara 70 bai yi wanka ba, a baya-bayan nan ya ba masana kimiyya mamaki kan yanayin cikar lafiyarsa.

An fara yin rubutu game da Amou Haji a shekarar 2014, inda aka yi masa lakabi da ‘Mutumin da ya fi kowane mutum dauda a duniya.’

A lokacin, yana zaune ne a wani karamin kauye da ke Lardin Fars na Kudancin Iran, yana rayuwa da cin naman dabbobin da aka kashe a hanya da shan ruwa mai dauda, kuma ya yi nesa da wanka, ana tunanin irin wannan rayuwar za ta iya sa shi rashin lafiya.

A lokacin da yake da shekara 80 a duniya kuma ga dukkan alamu yana cikin koshin lafiya, duk da rashin tsafta da yanayin rayuwarsa.

Kuma ga alama bai canja sosai ba, tun lokacin, yayin da wata kungiyar likitoci ta gudanar da gwaje-gwajen da suka nuna cewa yana cikin koshin lafiya.

Hotuna da labaran Amou Haji suna ta yawo a shafukan sada zumunta bayan da labarinsa ya fara yaduwa shekara bakwai da suka gabata.

Bayan haka, salon rayuwarsa yana da banmamaki. Aminiya ta taba kawo labarin wani Ba’indiye mai shekara 67 da ya shekara 38 bai yi wanka ba, sai ga alama Haji ya kasance wanda zai iya rike kambin duniya tare da shiga kundin tarihi na duniya a wannan bangare.

Idan da wani abu, na dan yi mamaki shi ne yadda Kungiyar Masana Kimiyya ta dauki tsawon lokaci tana bin diddigin mutumin tare da gudanar da wasu gwaje-gwaje a kansa don samun haske game da rayuwar mutumin da ya guje wa wanka shekaru da yawa, yana rayuwa a cikin kazanta.

Za a iya kwatanta shi da yanayin rashin tsabta sosai. Amma, sai a yi tsammanin mai irin wannan rayuwar ba zai kasance a raye ba.

Ayarin likitoci a karkashin jagorancin wani farfesa a fannin ilimin halittu, Dokta Gholamreza Molabi, daga Makarantar Kiwon Lafiyar Jama’a da ke Tehran sun ziyarci Amou Haji da ke kauyen Dejgah tare da shawo kan shi ya zo a yi masa wasu gwaje-gwaje.

Sun hada da gwaje-gwajen ciwon hanta da kanjamau da na kwayoyin cuta.

Dokta Molabi da ayarinsa sun yi sha’awar ganowa da yin nazari kan kwayoyin cuta da kwayoyin cuta da ka iya habaka a jikinsa wadda ba a wanke ta ba, amma sun yi mamakin ganin babu kwayoyin cuta da ke haddasa cututtuka, sai dai cutar da idan mutum yana cin abin da ya kamata a dafa a danye, cutar da aka samu ke nan a wajensa.

Kuma a bayyane bai haifar da alamun cutar ba.

Binciken ya kasance mai banmamaki musamman idan aka yi la’akari da cewa mai shekara 87 a kai-a-kai yana cin mussan dabbobin da aka kashe a kan titi kamar aladu da zomaye sannan, yana shan ruwan da ba a kula da tsabtarsa ba daga kududdufai ta hanyar amfani da gwana-gwanai masu tsatsa da ba a wanke ba, kuma an ba da rahoton cewa, yana zukar hayakin busassun kashin dabba idan bai samu taba a bututunsa ba.

Dokta Gholamreza Molabi ya yi imanin cewa sakamakon bincikensu game da gwajin shi ne, Amou Haji ya habaka tsarin garkuwar jiki mai karfi a tsawon shekaru da yawa da yake rayuwa a cikin mummunan yanayi.

Duk da lafiyarsa, Amou Haji ya sha fama da mugun nufi na ’yan uwansa, wadanda da yawa daga cikinsu suna yi masa ba’a, har ma suna zaginsa kan salon rayuwarsa.

A kwanakin baya ne Gwamnan yankin ya roki jama’a su bar shi da rayuwarsa ya ce, duk da kamanninsa, shi mutum ne mai sanyin hali wanda bai taba cutar da kowa ba