✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi Haihuwar Bakwaini

Ko haihuwar jarirai a watan bakwai zai iya kawo musu wata illa a rayuwa   Amsa: Eh, kuma a’a. Wato ya danganta da halin da…

Ko haihuwar jarirai a watan bakwai zai iya kawo musu wata illa a rayuwa

 

Amsa: Eh, kuma a’a. Wato ya danganta da halin da ya sa aka haifo jaririn a wata bakwai, da kuma kasa ko garin da aka haifo jaririn. Wato idan matsalar da ta sa aka haifo jariri ba a jaririn take ba, a mahaifiya ne, to da wuya jariri ya samu wata matsala a karan-kansa, cikin gilashi (’yar kwalba kamar yadda wasu sukan kira ta) mai dumi kamar mahaifa kawai za a sa shi ana shayarwa har sai an ga zai iya rayuwa ba a cikin gilashi ba. Amma idan matsalar da ta sa aka haifo bakwainin a jaririn take, to zai iya shiga hadari. Ka ga ke nan matsaloli da za su iya sa a haifi bakwaini za su iya zama ko dai a jikin mahaifiya ko a jikin jariri. Idan a jikin mahaifiya matsalar take babu matsala sosai, amma idan a jikin jariri matsalar take akwai damuwa, domin ciwon da ya fito da shi daga ciki zai iya yin ajalinsa tun kafin a je ko’ina. Sa’annan koda matsalar a jikin mahaifiya ce, shi jariri ba ya da wani ciwo ana hangen cewa zai iya shiga ’yan matsaloli na yawan ciwon ciki bayan an haife shi, ko yawan mura ko ciwon nimoniya, wadansu kuma sukan kasa samun girman jiki kamar sauran yara da suka kai wata tara a ciki.

Sai dai koda a jikin jariri ne matsalar take, a wasu kasashe inda kiwon lafiya ya ci gaba sosai, za su iya rainon wadannan jariri bakwaini, su kuma iya magance cututtukan da ke addabarsu. Kai in takaice maka bayani ma, ba bakwaini ba, ko a wata biyar aka haifi jariri a wasu kasashe kamar Sweden da Amurka da Jamus da Birtaniya, za a iya rainon jaririn yadda ya kamata a na’urori masu kama da mahaifa, jariri ya zamo tamkar a ciki yake. Kuma koda ciwo ne da shi za su yi iya kokarinsu su ga sun taimaka ya warke. Watakila ba ka taba jin wata tiyata da aka yi wa wani dan tayi a kasar Amurka wanda bai fi wata hudu ba, wanda aka fito da shi daga cikin mahaifa inda yake zaune, aka yi masa tiyatar cire wani kari aka mayar da shi ciki aka dinke, ya karasa watanninsa kafin a zo a haifo shi lafiya kalau? Wanda ya yi wannan tiyata likita ne dan asalin Najeriya da ke zaune a Amurka. Ka ga ke nan zancenmu ya tabbata cewa matsalar ta danganta da wurin da ta faru, idan ta faru a kasar da suke da kayan aiki, ba hadari amma idan ta faru a kasashe marasa kayan aiki a asibitoci, to komai na iya faruwa.

 

Me ke sa fitsarin mutum ya rika rabewa biyu? Amma ba ya zuwa da zafi?

Daga Aminu S. Kaduna

Amsa: Idan mutum ya ga fitsarinsa haka kawai na rabewa biyu alhali ba wani zafi ko zogi, alama ce ta cewa kamar akwai abin da ya toshe wani wuri ko yake neman toshe wani wuri a mafitsararsa. Yawanci abubuwan da kan toshe hanyar fitsari su ne tsofaffin miki na ciwon sanyi da ya shekara da shekaru a jiki ba a sha masa magani ba; wadansu kuma sakamakon mikin wani ciwo ne da suka ji sakamakon buguwa kamar ta hadarin abin hawa; wadansu kuma miki ne na ciwon wata ’yar tiyata da aka taba yi musu a hanyar fitsarin. Haka akwai dalilai da dama wadanda za su iya toshe mafitsara fitsari ya rabu gida biyu. Sai mutum ya je sun tattauna da likita ido-da-ido kafin a gano musabbabin aukuwar matsalar. Akan so mai irin wannan matsala ya samu ya je ya ga likita da wuri tun kafin mafitsarar ta toshe gaba-daya. Amma idan fitsarin ya zo da kansa ya daina rabuwa to ba matsala. Amma duk ranar da ya dawo ko da ya sake komawa daidai sai an ga likita. Wato idan abin ya zo fiye da sau guda, ko da ya koma daidai sai an ga likita kada mafitsara ta zo ta toshe gaba-daya abu ya zama imajansi.