✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi

Idan aka bar wa yara napkin da dangoginsa a jiki har suka daxe da fitsari da bayan gida a jikinsu, ko za su iya samun…

Idan aka bar wa yara napkin da dangoginsa a jiki har suka daxe da fitsari da bayan gida a jikinsu, ko za su iya samun wata illa?
 
 
Amsa: E, ai idan aka bar najasa a jikin napkin xin jariri ta fara daxewa shi da kansa zai isheki da kuka idan baki cire ba. Idan ma aka xauki lokaci mai tsawo kamar awowi shi bayan gidan kwayoyin cuta da ke cikinsa za su iya makalewa a fata su shiga karkashin fatar jariri su jawo maruru. Shi kuma fitsari gubar ammonia da yake xauke da ita ce za ta sa fatar wurin ta yi ja tana kaikayi tana wasu irin kuraje. Don haka kada a rika barin jariri a jike ko caba-caba cikin najasa, a rika saurin dubawa ana canzawa.
 
Wai da gaske ruwan nan na gripe water mai rage kumburi a jikin jarirai daidai yake da ruwan sha na roba. Idan ba haka ba ne mene ne bambancinsu. Wanne ya fi dacewa a ba jariri?
Daga Usman Muazu, Funtua
 
Amsa: A’a haba Mallam Usman, kada ka dawo da karatun baya mana. Wane ruwa kuma kake ba jariri. Ai mu a nan ba a ba jariri kowane irin ruwa sai ya kai watanni biyar zuwa shida sai dai ruwan magani. Shi wancan ruwan gripe water ma da kake magana akai a da ne aka rika ba wa jarirai masu samun kumburin ciki, amma yanzu an gano ba shi da wani amfani a likitance.
 
Wai da gaske ne ciwon sanyi na mara zai iya hana haihuwa?
Daga Ahmad M. Borno
 
Amsa: E, da gaske ne. Ba a mace ba, ba a namiji ba, duk ciwon sanyin da ya daxe a jiki ba a yi maganinsa ba karshensa ya sa miki a mafitsarar namiji ko mahaifar mace ta yadda dukansu za su kasa haihuwa. A maza alamun da farko sune na ganin farin ruwa da zogin fitsari kafin a zo a kasa fitsarin idan hanyar ta toshe. A mata akwai ciwon mara mai tsanani da ganin ruwa da rikicewar al’ada da kasa haihuwa saboda rikiccewar al’adar da samun miki. Amma za a iya aiki na tiyata a buxa hanyar a duka macen da namijin. Tun kafin ma a kai wannan lokacin da mutum ya ji alamun ake so ya je asibiti a bashi maganin da zai warkar da matsalar kafin ta yi wannan barnar.
 
Matata ce ke samun matsanancin ciwon mara a yayin al’ada. Shi ne muke neman mafita.
Daga Isyaku Malumfashi
 
Amsa: Idan mace na fama da matsanancin ciwon mara na al’ada magungunan kashe zogi za ta nema waxanda za a iya samu ko da a kyamis ne ba komai. Idan ta yi amfani da su ba sauki to shi ne sai an haxa da zuwa asibiti an ga likitan mata domin a duba dalili, a ba da magani mai xan karfi.