Mace ce mai juna biyu amma bai wuce mako biyu a haihu ba sai aka yi gwaji ya nuna jininta maki 26. Ina mafita?
Daga Umman Abdul
Amsa: Jinin ya dan yi kasa kadan. Mafita ita ce ta bi shawara da duk abin da likitan da ya bukaci a yi wannan awon ya ce. Mafi muhimmanci ya kasance ta haihu a asibiti don a dauki dukkan matakan da suka dace.
Matata tana da ciki wata daya za ta iya fara awo?
Daga Alhaji Jinjiri Mil 12
Amsa: Eh, za a iya farawa. Ya ma fi kyau a fara da wuri.
Mace mai juna biyu wata biyar amma ruwan nono ya fara zuba. Shin hakan ba matsala?
Daga Amatulla A. A
Amsa: A’a ba matsala, ai dama ana fara sarrafa ruwan nono da ciki ya yi rabi wato tun daga wata hudu da samun ciki. A wadansu zai iya fara zuba tun kafin haihuwa, a wasu kuma sai an haihu.
Da gaske yawan shan lemon kwalba na 7UP zai iya hana daukar juna biyu?
Daga A.B.A Gangare
Amsa: A’a shaci-fadi ne ba kanshin gaskiya a zancen
Me ke kawo yawun barci? Mene ne maganinsa? Ko na wanke bakina idan zan kwanta da na yi barci zai zubo
Daga Maman Islam
Amsa: Ba ciwo ba ne zubar miyau idan ana barci, bambancin halitta ce wadda wadansu da dama ke samu. Kada abin ya daga miki hankali in dai ba maigidan ne ya kosa ba. To in dai haka ne za a iya cewa za ki iya samun irin takunkumin nan na fuska mai daure haba irin na masu minshari da muka taba sa hotonsa. Za ki iya samunsa a manyan kyamis, ki rika daure habar lokacin barci don kada miyau ya gangaro kan matashi. Duk wasu magunguna da za a ba ki, za su kamar miki da miyau ne, baki ya bushe kamas, wanda ba za ki so ki dandana hakan ba.
Yarona ne sai ya yi ta kuka yana cewa kafarsa tana ciwo daga kwauri. Ko mene ne mafita?
Daga Usman 440 Funtuwa
Amsa: Idan dai ba buguwa ya yi ba, wanda za ka iya dubawa ko ka kai shi likita ya duba, watakila ma a yi hoto, in komai daidai ne, aka ba shi maganin zogi zai bari. Sa’annan yana da kyau yara wadanda ba sa samun abinci masu gina kashi a kullum, abinci irin su madara da kwai masu sinadarin calcium da bitamin na ajin D, a rika saya musu bitaman masu calcium da bitaman na D su rika sha jefi-jefi domin rage ciwon kashi da kiyaye ciwon gwame