✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin Tambayoyi

Me za a ba jaririn da ba ya girma? Bayan ruwan nono akwai magani da za a iya ba wa jaririn da ba ya kiba?…

Me za a ba jaririn da ba ya girma?

Bayan ruwan nono akwai magani da za a iya ba wa jaririn da ba ya kiba? Makonsa biyu da haihuwa sai aka ce mini ko na sayo maganin wankin ciki.

Daga Baban Muhammad da Ameera Azare

 

Amsa: A’a, kada a ba shi komai, sai ruwan nono, kada a sayo wani magani. Jaririn da ba ya kara kiba karin ruwan nono yake bukata domin watakila ba ya koshi ke nan, ko kuma ruwan nonon ba ya zuwa da yawa.

Da fari dai ya kamata ka sani cewa da wuya ka gane kibar jariri a cikin mako biyu kacal da haihuwa, sai dai ko bayan wata, domin an kiyasta cewa akalla duk mako jariri ya kamata ya kara nauyin giram 150-250 wato kwatankwacin kwatan kilo, ko kuma ka ce a wata ya kara kilo guda. To in dai ba ma’aunin nauyi ne da kai a gida ba, da wuya a cikin mako biyu a fahimci inda ya sa alkibla.

Idan ba ka da abin awon nauyin, abin yi yanzu shi ne, sai ka je inda za a iya auna nauyinsa na zahiri kamar a karamin asibiti idan kun je allura, a auna nauyinsa a fada maka. Sai ka kawo nauyinsa na haihuwa ka cire daga cikin abin da aka fada maka. Misali idan nauyinsa na haihuwa kilo uku ne sai yanzu aka auna aka ga kilo uku da rabi, wato maki uku da digo biyar ke nan. To rabin ke nan ya kara tsawon makonninsa a duniya, wanda hakan ba matsala sosai. Amma idan abin da ya kara bai wuce digo biyu ba, to sai an dauki mataki.

Matakin kuwa shi ne na kara masa yawan nono, ta yadda za a rika ba shi ruwan nono duk bayan awa daya zuwa awa daya da rabi ko bai nema ba, idan kuma barci yake a dan bar shi sai bayan awa biyu zuwa uku tunda su jarirai sai su kai awa 14 ko ma fiye suna barci, amma  yawanci a rarrabe. Ko kuma idan jaririnku bai da karfin tsotso, kamar bakwaini sai an dage an matso a kofi a ba shi da sirinji. Ko kuma idan haihuwar fari ce, sai an koya wa mahaifiyar yadda ake shayarwa.

Idan kuma mahaifiyar tana tunanin babu ruwan nono ne to ita ma sai ta dage da ci da sha sosai, musamman abubuwa masu ruwa-ruwa, ci ba sau uku ba, kamar sau biyar zuwa shida ma a rana idan za ta iya.

Idan kuma duk an yi haka an ga ba ruwan nono kuma nauyi ba ya karuwa to wannan gaba sai an kara da madarar jarirai ta gwangwani, ba magani ba. Haka za a yi ta yi har wata shida, lokacin da za a iya fara ba shi ruwa da abinci mai dan ruwa-ruwa ko taushi-taushi bayan ruwan nono.

To ka ji duk a wannan zancen babu maganar magani a ciki, sai dai fa idan kuma akwai alamun ciwo, kamar zazzabi ko amai ko gudawa ko kin karbar nonon kwata-kwata, ko yawan kuka, to wannan kuma dole sai likita ya duba shi ya tabbatar sai ya ba a maganin.