Na yi ciki na fari na samu hawan jini da jijjiga, aka yi tiyata na samu jariri. Na biyu da kaina na haihu amma dan ba rai. Ga na uku ina shayarwa. Ko idan na dauki wani juna biyun yanzu ba zai zamo matsala ba?
Daga A. Tofa
Amsa: Hajiya saurin me ake? Ko kuma in ce da wa ake takara? Ko da baki da wannan tarihi na matsaloli shi kansa lafiyayyen ciki ma zai iya zama matsala ballantana kina da irin wannan tarihi na hawan jini da jijjiga da tiyatar C.S da komawar da, a jere, duka ke kadai.
Amma idan kin nace shawarar da zan ba ki ita ce ki samu asibiti inda kwararriyar/kwararren likitan mata take, ko da na kudi ne, ki je ki ji shawararta ki saba ta rika bibiyarki. Abin dai nufi shi ne, za ki iya gwadawa in dai a gaban kulawar irin wadannan kwararrun likitoci ne.
Ni ma matata tunda ta samu jijjiga aka yi mata tiyatar haihuwa (C.S) take samun ciwon baya da faduwar gaba. Mun je asibiti an sha magani amma har yanzu abin ya ki.
Daga A.J., Mil 12
Amsa: Kai ma ina jin sai kun hada da babban asibiti bangaren zuciya inda za su duba zuciyar a tabbatar ba tabuwa ta yi ba daga ciwon hawan jini da jijjiga. Ma’ana akwai gwaje-gwaje da za a yi musamman na zuciya ba kawai magunguna ba.
Idan ina shan magungunan karin jini kamar chemiron nakan samu taurin bayan-gida ya kuma koma baki-kirin. Ko hakan matsala ce?
Daga B.T
Amsa: A’a ba matsala ba ce, magungunan karin jini suna iya sa haka. Kawai dai ki tabbatar ba da ka kike sha ba, an ba ki ne a asibiti an kayyade miki lokaci, kuma kina bibiyar likitan da ya ba ki. Sai kuma ki rika yawan cin kayan itatuwa da na ganyaye domin ciki ya rika saki.
Sai tambayar Abdullahi A. Kotagora, wadda za a saya. Amsarka Malam Abdullahi ita ce cewa hakan da kake tambaya a kai matsala ce wadda sai kun je an duba, akwai abubuwa da dama masu sa haka.