Matata duk lokacin da ta gama al’ada sai jininta ya yi kasa. Mun je asibiti, amma har yanzu hakan tana faruwa. Ko mece ce shawara?
Daga Muhammad Bello, Kano
Amsa: Da ma mata kan fi maza karancin jini a jika saboda al’ada. To amma ita al’adar yau-da-kullum a karan-kanta ba ta sa karancin jinin da zai cutar, har ya yi kasa sosai ya fara kawo alamun rashin jini, sai fa idan akwai wani abu ba al’adar kadai ba. Wato ko dai kwanakin al’adar na wuce misali ko yawan zubarta na wuce misali, ko ba ta iya cin abinci sosai, ko kuma ba ta samun abincin mai amfani sosai, ko kuma ma akwai wani ciwo na daban a jikinta. Don haka ke nan sai dole an gano mene ne dalili a asibiti. Idan ba su gano dalili ba su ba ku takarda zuwa wani asibiti babba inda za a gano dalilin.
Mene ne sahihancin bayanai cewa za a rika bi gida-gida ana raba ragar sauro a kuma ba yara ’yan shekara daya zuwa biyar magunguna ko allurai na kiyaye zazzabin?
Daga Aminu S.
Amsa: Idan hakan ya zo garinku to ba mamaki, tunda ba ka fadi inda kake ba. A ’yan shekaru biyun nan da suka wuce ne hukumomi tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya suka fara wannan kokarin a Jihar Barno domin rage yawan mace-macen yara ’yan kasa da shekara biyar saboda a rage musu radadin cututtukan zazzabin cizon sauro, tunda da ma suna fama da tashe-tashen hankula da ma yunwa.
A tsarin, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya ta fito da shi, za a rika ba wa yara ’yan kasa da shekara biyar magungunan ciwon maleriya a watannin damina, ko yara na da ciwon ko ba su da shi, a matsayin hanyar kariya daga cutar. Domin an lura cewa yara sun fi mutuwa daga cutar maleriya fiye da kowace cuta, a kuma watannin damina mutuwar ta fi yawa. Wadannan magunguna ne na kariya (wato magungunan da dama ake ba mai ciwon) ba alluran rigakafi ba kamar yadda aka fara gwaji a wasu kasashe a Afirka (wato Malawi da Kenya da Ghana).
Tunatarwa a kan alluran rigakafin yara
Daga Garba Adamu, na Karamin Asibitin Matsango, Azare
Yaron da aka haifa a asibiti, a take za a yi masa allurai biyu; ta ciwon hanta da ta tarin fuka. Sai digon-bakin shan inna daya. Daga nan sai zuwa na biyu a mako na shida inda za a yi alluran cututtuka bakwai; ciwon hanta, sarke-hakora, hangum, tarin shika, agalawa da ta danshin huhu/ciwon kunne, sai ta gudawa. Sai digon bakin shan inna na biyu. Daga nan sai zuwa na uku a mako na 10, inda za a maimaita abin da aka yi a mako na shida. Daga nan sai zuwa na hudu a mako na 14, inda nan ma maimaici ne. Zuwa na biyar lokacin yaro na watanni shida, digon bakin sinadarin bitamin A mai kara karfin gani zuwa na karshe, lokacin yaro ya kai wata tara, akwai alluran cutttuka biyu, na kyanda da shawara.