✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi

Ina da tsohon ciki, to rannan sai na fadi na bugu sosai. Yanzu bayana da kafadata ke min ciwo. Ko hakan matsala ce kenan wadda…

Ina da tsohon ciki, to rannan sai na fadi na bugu sosai. Yanzu bayana da kafadata ke min ciwo. Ko hakan matsala ce kenan wadda za ta sa a yi hoto?

Daga Maman Yasir

 

Amsa: A mafi yawan lokuta idan mace mai juna biyu ta fadi ta bugu akan kyautata zaton abinda ke ciki ma na samun buguwa, musamman a dan tayin da ya girma, kamar yadda kika ce kema naki tsohon ciki ne. Idan mace mai juna biyu ta bugu irin buguwar da ba za a ce ta yi gaggawar zuwa asibiti ba, wato ba ta ji jiki sosai ba, sai ta saurara ta ji ko motsin jariri a ciki ya ragu ko ya karu, ko kuma yana nan yadda yake da ko ma ya daina motsi. karuwar motsi da raguwar motsi alamu ne na cewa shi ma jariri ya tabu. Daina jin motsi ma abin na nufin buguwar ta yi munin da sai an garzaya imajansi. Amma idan motsinsa na nan kamar da za a iya bari har sai ranar awo ta zagayo a je a fadawa likita ya/ta duba sosai a yi hoto. 

 

Ni ina da juna biyu amma idan na je tsuguno ko fitsari ne sai na ga zubar jini ta baya ba ta gaba ba. Ko hakan zai iya shafar juna biyun? Kuma wane irin ciwo ne haka?

Daga Mariya.

 

Amsa: E, wannan da alama basur ne yake zubar miki da jini. Yana da hadari a ce mutum na da basur mai zubar da jini ballantana a ce a mai juna biyu wadanda dama jininsu sukan sanwa abinda ke ciki. Don haka wannan zai iya sa miki ciwon karancin jini mai hadari idan baki je an duba an baki magani ba.

 

Me ke kawo kurajen gumi a lokacin zafi a yara?

Daga Yaana Garba Gashuwa

 

Amsa: Ga shi nan kuwa kin fada. Zafi shine ke kawo kurajen gumi. Fatar wurin da ke yawan yin kurajen zafi sun fi son wurin a bushe da sanyi-sanyi. A mafi yawan lokuta barin fitsari ya dade shima yana taimakawa wurin ya kara zafi da danshi da kuraje. Akwai mayukan shafawa a kantuna ma ba dole sai kyamis ba, da akan shafawa yara domin kiyaye hakan, irinsu sudocrem, wanda za a shafa kafin a nadesu da napkin, yakan kiyaye kuraje ko na fitsari ko na zafi.

 

Na yi bari watanni uku da suka wuce amma har yanzu ba na jin dadin jikina – ciwon kafa zubar jini da rashin karfin jiki da rashin iya tafiya. Na je asibiti bayan barin an ce ba ni da matsala, shine nake neman shawara.

Daga Maman Khadija, Gusau

 

Amsa: Ai tsakanin lokacin da aka duba ki watanni uku da suka wuce zuwa yanzu labari ya canza, don haka ki fara azamar komawa ko ma ki nemi wani asibiti mai dan girma sama da na fari, domin  tabbas ba lafiya ba.