✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

La’eeb: Abin da dan aljanin Gasar Kofin Duniya na Qatar ke nufi

Bisa ga al'ada ta gasar duk kasar da za ta karbi bakunci, ta kan tsara na ta dan aljanin.

A ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022 za a fara gasar Kofin Duniya a kasar Qatar, wadda tuni ta shirya tsaf don karbar bakunci.

Bisa ga al’adar gasar Kofin Duniya, duk kasar da ta za ta karbi bakunci, takan yi amfani da dan wani aljani (mascot) wanda gidajen talabijin da sauran kafofin sadarwa za su yi amfani da shi wajen bayyana al’ada, tsari da jadawalin yadda gasar za ta kasance a kasar da ke karbar bakuncin gasar.

Kamar sauran masu karbar bakuncin gasar, Qatar ta fitar da nata dan aljanin wanda ta yi masa lakabi da ‘Laeeb’, wato hazikin dan wasa.

An yi amfani da La’eeb wajen fayyace shiga, tsari da irin al’adar mutanen kasar Qatar.

Tuni aka fara amfani da dan aljanin a allunan talla, gidajen talabijin da sauran kafafen sadarwa na intanet da sauransu gabanin fara gasar nan da mako biyu masu zuwa.

La’eeb ba wai yana bayyana abin da ya shafi kasuwanci da harkar kwallon kafar kasar Qatar ba ne kadai, a’a har da abin da ya shafi tsarin rayuwar mutanen da suka karbi bakuncin gasar.

La’eeb

An dai fara zayyana dan aljanin da ke zaman tambarin Gasar Kofin Duniya ne a shekarar 1966 yayin da Ingila ta karbi bakunci a wancan lokaci.

Tun daga lokacin masu masaukin bakin gasar suka ci gaba da kirkira da kuma amfani da shi wajen fayyace irin al’adu da dabi’un al’ummar kasashensu da ke karbar bakuncin gasar.

Kasashe irin su Mexico, Jamus, Argentina, Sifaniya, Italiya, Amurka, Faransa, Koriya ta Kudu da Japan, Afirka ta Kudu, Brazil da Rasha dukkaninsu sun kirkira sun kuma yi amfani tambarin da ya zama alamar gasannin da suka karba.