Dole ’yan jarida da dama, musamman masu aiki a gidajen rediyo da talabijin na Arewacin Najeriya, su mike tsaye idan suka ga Farfesa Ladi Sandra Adamu.
Dalili kuwa shi ne in dai a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya suka yi karatu, to akwai yiwuwar sun sha daga koramarta ta ilimin aikin jarida.
- Tauraruwar Arewa: Watan girmama matan Arewa ya tsaya
- Haba kungiyar ASUU, a rika sara ana duban bakin gatari
Kai ko da ba a ABU suka yi karatu ba, ta yiwu sun taba amfana da wata makala ko wani rubutu da ta yi – fiye da rubuce-rubuce 800 da aka yi a kan aikin jarida a fadin duniya ne suka ambace ta a matsayin mabubbugar ilimi da ake barar a cikinsu.
Ban da wannan ma, Farfesa Ladi Sandra Adamu ce farfesa ta farko a fannin aikin rediyo da talabijin a Arewacin Najeriya.
Haka kuma ta rike mukamin shugabar gidan rediyon tsangaya na ABU Campus FM har tsawon shekara 10.
Kafin nan kuma ta taba rike mukamin Mataimakiyar Edita a kamfanin jaridar The Democrat da ke Kaduna.
Farfesa ta farko a rediyo da talabijin
Ta kuma rike mukamin Editar Labarai a gidan talabijin na kasa, NTA, a Jos, da kuma Jami’ar Hulda da Jama’a ta Ofishin Jakadancin Najeriya a Atlanta, Amurka.
Farfesa Ladi Sandra Adamu ta yi karatunta ne a Jami’ar Birnin Landan (City University London) da Kwalejin Colombia da ke Los Angeles a Amurka, da Jami’ar Loyola Marymount, a Los Angeles, da Cibiyar Golda Meir da ke Haifa, Isra’ila, da kuma Jami’ar Ahmadu Bello.
Turaruwar tamu ta yau ta samu lambobin girmamawa da dama, ciki har da ta baya-bayan nan wadda Kungiyar Masu Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya ta ba ta saboda tana daya daga cikin mutanen da suka fi bayar da gudunmawa ga bunkasar aikin jarida a gidajen rediyo da talabijin.
Wani abu kuma game da Farfesa Ladi wanda ba kowa ne ya sani ba, shi ne: wakar da Marigayi Mamman Shata Katsina ya yi wa Adamun Pankshin, wato mahaifinta.