✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarun da suka yi tambari a Najeriya a 2020

Manyan labarun da suka dauki hankali a Najeriya a shekarar 2020

Shekarar 2020 ta kasance ta musamman ta fuskoki da dama a Najeriya da ba za a iya mantawa ba.

Hakika za a dauki tsawon lokaci ana yin bayani idan aka ce za a lissafo ilahirin muhimman abubuwa ko labarun da suka dauki hankalin a shekarar.

Labarun 2020 sun shafi bangarori daban-daban na rayuwa kuma sun hada da na al’ajabi, jarumta, takaddama, badakala, ta’addanci da sauransu.

Ga wasu da Aminiya ta tsakuro daga shekarar mai yin bankwana:

  1. Coronavirus

An shafe kusan daukacin shekarar 2020 ana labarai a kan cutar coronavirus wadda ta fara bulla a kasar a watan Fabrairu ta wani dan Italiya da ya shigo kasar.

Dubban mutane sun kamu, daruruwa sun rasu sakamakon cutar da ta jawo sanya dokar hana fita da rufe makarantu da kasuwanni wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a na tsawon watanni a matsayin matakin hana yaduwarta.

An rufe iyakokin Najeriya, yayin da cutar ta jawo faduwar farashin mai a kasuwannin duniya baya ga asarar biliyoyin kudade ga kashe wurin samar da kayan kariya da gwajin cutar da kuma bayar da tallafi.

Wasu mace-mace masu yawa da aka samu da suka tayar da hankali a Jihar Kano ma an danganta su da cutar, duk dacewa Kwamitin Binciken mace-macen da Gwamnatin Jihar ta kafa ya karyata ikirarin na Gwamnatin Tarayya

A halin yanzu Najeriya na daukar matakan kare yaduwarta a karo na biyu, yayin da wasu kasashe ke fama da sabuwar na’in cutar da ake kokarin ganin rigakafinta ya wadatu a duniya.

Coronavirus: 13 sun warke, 5 sun mutu a Edo
Daya daga cikin likitocin da ke kula da majinyata a daya daga cikin wuraren killace masu ccoronavirus.
  1. Kisan gillar Zabarmari

Mayakan Boko Haram sun ritsa manoma a gonaki suka yi ta fille musu kai, wasu kuma suna musu yankan rago a yankin Zabarmari na Jihar Borno, aika-aikan da ya sha Allah-wadai daga sassan duniya.

An samu alkaluma masu cin karo da juna na adadin mutanen da kungiyar ta kashe: hukumomi suka ce mutum 43 ne; Majalisar Dinkin Duniya ta ce sun fi mutum 110; yayin da kungiyar Boko Haram ta ce 78 ne.

Zulum yana taimakawa wajen ajiye gawa
  1. ‘Gwamnan Arewa ne Shugaban Boko Haram’

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafia ya yi zargin cewa wani gwamna a Arewacin Najeriya ne Kwamandan kungiyar Boko Haram.

A hirar da gidan rediyon Nijeriya Info ya yi da shi, Mailafia wanda ya ce yana cikin masu tattaunawa da tubabbun ’yan Boko Haram ya kuma ce kungiyar na hada kai da ’yan bindiga suna safarar makamai da kudade da sauran abubuwa domin tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Daga baya dai ya karyata kansa tare da neman afuwa, inda ya ce wasu da ya hadu da su a kasuwar kauye ne suka fada masa abubuwan da ya fada a hirarsa da gidan rediyon.

Kalaman nasa dai sun jawo masa gayyata daga ’yan sanda da hukumar tsaro ta DSS yayin da aka yi ta kiraye-kiraye da cewa a binciki zargin a hukunta masu laifi, shi kuma gidan rediyon aka yi masa tara saboda yada bayanan karya.

Obadiah Mailafiya, Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN)
  1. Zaben Sarkin Zazzau

Tirka-tirka ta dabaibaye zaben Sarkin Zazzau na 19 tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da Masu Zaben Sarki a Masarautar Zazzau, wadanda bayan sun tantance ’yan takara sun mika wa gwamnati zabinsu na mutum uku bisa al’ada, Gwamnan El-Rufai ya umarce su da su sake, don ba wa karin ’yan takara dama; suka sake suka kuma mika sunayen mutanen da suka zaba a karon farko.

Ce-ce-ku-ce ya dabaibaye zaben Sarkin musamman bayan da gwamnan ya ce yana karatun litattafan tarihin Masarautar, inda aka zargshi da neman nada dan lelensa wanda kuma ba ya cikin mutum uku da Masu Zaben Sarki suka zaba.

Daga karshe dai gwamnatin jihar ta ayyana ta kuma nada Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau na 19, al’amarin da Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu, wanda ya fi samun kuri’u daga cikin mutum uku da Masu Zaben Sarki suka zaba, ya kalubalanta a gaban kotu.

Ana nan ana ci gaba da shari’ar da ya shigar ta namn kotu ta sa a nada shi Sarkin Zazzau, tunda Ahmad Bamalli ba ya cikin wadanda aka zaba.

Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli
Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli
  1. Auren Ba’amurkiya

Labarin wani matashi a Jihar Kano da ya auri wata mata da ta niki gari daga Amurka zuwa Kano saboda masoyin nata ya karade kafafen labarai.

Yawan shekaraun Janine, wadda ta kusa ninka na angonta Suleiman; kasancewarta Ba’amurkiya; bambancin al’addu; amincewar iyayen matashin wanda ke shekararsa ta biyu a jami’a; komawarsa Amurka bayan auren; da sha’anin addini na kadadan daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin jama’a.

Zuwan Janine Kano biyu saboda batun aurenta da Suleiman, karon farko aka tattauna aka daidaita, karo na biyu kuma aka kammala shirye-shirye aka kuma shafa Fatihar auren ma’auratan da hotunansu suka yi tashe.

Suleiman da amaryarsa Janine Ba’amurkiya
  1. Yajin aikin ASUU

An shafe wata 10 ana kwan-gaba-kwan-baya tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) wadda ta fara yajin aiki tun a watan Maris domin neman gwamanti ta cika alkawurin da ta yi wa malaman tun a shekarar 2009.

A yi ta hawa kan teburin sulhu ba tare da samun daidaito ba, yayin da masu ruwa da tsaki ke neman ganin an kawo karshen yajin aikin an koma makarantun da ake zargin rufe su ya taka rawa wurin tarzomar da matasa suka yi ta EndSARS a lokacin.

A watan bangarorin suka sasanta ASUU ta janye yajin aikin bayan gwamanti ta biya abin da ta ce sama da kashi 95 na bukatun malaman na biyan kudaden da suke bin ta bashi da kuma tsame su daga tsarin albashin bai-daya na IPPIS wanda suke zargi akwai cuta a ciki.

  1. Yaron da aka daure a turken dabbobi

A 2020 aka ceto wani karamin yaro da kishiyoyin mahaifiyarsa suka daure shi shekara biyu a turken awaki a Jihar Kebbi.

Makwabta ne suka tsaigunta wa masu kare hakki, su kuma suka dauko ’yan sanda suka je aka kubutar da yaron da Gwamnatin Kebbi ta dauki nauyin ci gaba da kula da shi, aka kuma fara binciken kishiyoyin mahaifyar yaron tare da mahaifinsa.

Daga baya an yi ta samun kananan yara, matasa, magidanta da matan aure wadanda kishiyoyin iyayensu, ’yan uwansu, ko mazajensu suka yi wa irin wannan dauri saboda dalilai daban-daban da hukumomi suka rika kubutarwa.

  1. Daukar ma’aikata 774,000

Shirin daukar kananan ma’aikatan wucin-gadi na Gwamantin Tarayya na daga cikin labaran da suka yi tashe a 2020, musamman bayan takaddama ta yi masa dabaibayi.

Daukar ma’aikatan da za su yi aikin wata uku kacal ya haifar da zazzafar cacar baki tsakanin Majalisar Tarayya da Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo, wanda shirin ke karkashinsa, har Majalisa ta dakatar da daukar ma’aikatan shi kuma ya ce ba ta isa ba ta hana shi yin abin da Shugaban Kasa ya sa shi.

Jijiyoyin wuya sun tashi tsakaninsu ne a lokacin da kwamitin Majalisar ke sauraron bahasin shirin, inda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Samar da Ayyuka (NDE) Nasir Ladan ya ce Keyamo ne ke kidansa yake rawansa a daukar ’yan kwamitin tantance masu neman aikin.

Tun da farko dai an samu tankiya kan wanda zai jagoranshi shirin wanda NDE za ta kula da shi tsakanin Ladan da kuma Keyamo wanda hukumar ke karkashin ma’aikatarsa.

  1. Zanga-zangar EndSARS

Zanga-zangar EndSARS da aka fara a watan Oktoba ta jima ana jin amonta, ba ma a Najeriya kadai ba, har a fadin duniya, inda ta kai ga har sai da Twitter ta yi wa maudu’in #EndSARS tambari na musamman.

Masu zanga-zangar neman a rushe sashen ’yan sanda na SARS mai yakar ayyukan fashi ta karade Najeriya, tare da tsayar da harkoki a sassan kasar musamman a yakin Kudanci.

Sai da ta kai ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta rushe SARS ta kuma ce za ta yi wa jami’an sashen gwajin kwakwalwa kafin ta ba su wani aiki; Shugba Buhari da kansa ya fito ya amsa bukatun da masu zanga-zangar.

Masu zanga-zangar #EndSARS

Zanga-zangar rikide zuwa tarzoma inda bata-gari suka rika kashe fararen hula da jam’ain tsaro suna sace makamai; kona kayan gwamanti da na jama’a; fasa gidajen yari ana sakin fursunoni; fasa shaguna, gidajen mutane da ma’adnan gwamnati ana satar kaya da sauransu.

Lamarin ya kazance ne washegarin zuwan zuwan sojoji da suka yi harbi  domin watsa taron masu zanga-zangar da suka taru a unguwar Lekki, Jihar Legas bayan gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita.

An yi ta zargin sojoji da kashe masu zanga-zangar, zargin da suka karyata. A halin yanzu dai kwamitocin sauraron korafi da yin sulhu kan rikicin jihohi daban-daban na kan gudanar da aikinsu.

  1. Badakalar NDDC

Binciken zargin watandar biliyoyin Naira na kwangila da tallafin COVID-19 a hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) na daga cikin labarun da suka yi kaurin suna a 2020.

Yayin da kwamitin Majalisar Tarayya ke zargin hukumar da yin watsi da daruruwan ayyuka tare da yin wa-ka-ci-kata shi da kudade, Minstan Hukumar, Godswill Apkabio ya zagi ’yan Majalisar da karbar kwangiloli daga hannunta, lamarin ya kai ga Shugaban Kwamitin ya janye daga jagorantar zaman.

Yawancin kwangilolin an biya kudadensu, har da kari, amma an yi watsi da su, kuma ’yan Majalisar sun musanta zargin suka nemi Akpbio ya kawo hujja ko su sa a daure shi kafin daga baya ya ce an yi wa bayanin da yayi gurguwar fahimta.

Ana tsaka da zaman sauraron bahasi a gaban Majalisar zargin badakalar ce mukaddashin shugaban hukumar, Farfesa Kemebradikumo Pondei ya yanke ciki ya sume.

Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio lokacin zaman kwamitin Majalisar Wakilai
  1. Sace daliban Kankara

Najeriya da ma duniya ta girgiza bayan mahara sun yi sace dalibai 344 a Makarantar Sakandaren Kimmiyya ta Gwamnati (GSSS) da ke Kankara, Jihar Katsina bayan musayar wuta da ’yan sandan a makarantar.

Yayin da iyayen daliban suka yi zaman dirshen a makarantar, an yi ta samun alkaluma masu karo da juna tsakanin gwamnati da masu bincike game da adadin yaran da maharan suka sace.

Bayan gwamnati ta ce ’yan bindiga ne suka dauke yaran, tana kuma tattaunawa da su domin sako yaran, sai ga shi kungiyar Boko Haram ta fito tana ikirarin cewa mayakanta ne suka sace yaran, wanda bayan shi aka fitar da bidiyon ikirarin sace daliban daga kungiyar.

Daga baya dai an sako yaran, wadanda su da gwamnati suka tabbatar cewa ba ’yan Boko Haram ba ne suka sace su ba.

Daya daga ciki daliban da ya yi magana a cikin bidiyon
  1. Karin farashin mai da fetur

Karin farashin man da aka sanar tare da cewa gwamanti ta tsame hannunta daga sanya farashin mai ya karade Najeriya, inda aka yi ta sukar matakin.

Kwanaki kadan ne tsakanin karin farashin man da na wutar lantarki wanda ya shi ma ya sha suka, duk da cewa Hukumar Kula da Lantarki ta Kasa (NERC) ta ce masu samun wuta na sama da awa 12 ne kadai karin ya shafa.

Najeriya ta kuma yi fama da karuwar farashin kayan masarufi musamman bayan ambaliyar da ta yi barna

Makonnin kadan bayan nan ne aka sanar da rage farasahin mai, karo na biyu da hakan ke faruwa yayin da sau biyar aka kara farashin a mai a cikin shekarar.

Yadda karancin Man Fetur ya hada cunkosun ababen hawa

 

  1. Ambaliyar ruwan sama

Ambaliyar ruwan sama a damuwar bana ta hadda asara mai dimbin yawa na rayuwa, dukiyoyi da amfanin gona da sai dai a kiyasta a sasan Najeriya.

Ambaliyar ta zo ne a yayin da manoma da gwamnatoci ke kyautata fatar samun amfani mai yawa da riba da zai kai ga samar da isasshen abinci a cikin gida.

Sai dai irin asarar da aka tafka ta kai ga sai da Gwamantin Tarayy ta shiga bayar da tallafi ga mutanen abin ya shafa.

Wasu daga cikin gonakin da ruwa ya mamaye a Karamar Hukumar Argungu ta Jihar Kebbi
  1. Maisiket

Wani labari da ya tayar da kura shi ne na wani matashi da dubunsa ta cika bayan ya yi wa mata akalla 40 fyade a garin Kwanar Dangora, Jihar Kano.

Da tsakar dare ne ’yan banga suka yi masa kofar rago suka cafke shi tsirara bayan an fatattake shi daga wani gida da ya yi yunkurin shiga domin tafka ta’asar tasa.

Maisiket  (sunan da mata suka yi wa lakabi saboda yadda ya addabi garin) ya shaida wa ’yan banga cewa ya yi wa mata akalla 40 a garin fyade, cikinsu har da kananan yara da tsofaffi.

Wata dattijuwa mai shekara 80 da ta bayyana murnarta da cafke, ta shaida wa Aminiya cewa Maisiket ya yi mata fyade har da raunuka bayan ya sumar da ita, ya kuma washe mata ’yan kudade.

Tsohuwar da Mai Siket ya yi wa fyade
  1. Tir-tirkar Rahama Sadau

Jarumar masana’antar Kannywood Rahama Sadau ta karade shafukan labaru bayan wani hoto da ta wallafa a shafinta na Twitter ya kai ga wani mai tsokaci a kai ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW).

An dauki tsawon lokaci ana muhawara a kan batun batancin, duk da cewa ba ta bata lokaci wurin cire hoton ba.

Duk da haka sai da ta fito ta bayar da hakuri da cewa ba da niyyar abin da ya faru ta wallafa hoton ba.

Gabanin nan, labarin Rahama yi tashe a 2020 a lokacin kaddamsar da fim din Mati A Zazzau, wadda take daya daga cikin jamruman fim din.

Rahama Sadau a lokacin da take ba da hakuri ga al’ummar Musulmi