✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Nura: Yadda kilu ta janyo bau

Assalamu Alaikum. A yau na kawo muku ci gaban labarin Nura, wanda na fara a makon jiya. Idan ba ku manta ba, na tsaya ne…

Assalamu Alaikum. A yau na kawo muku ci gaban labarin Nura, wanda na fara a makon jiya. Idan ba ku manta ba, na tsaya ne a inda Nura yake rokon mahaifinsa da ya bar shi ya zama mahaddacin kur’ani domin shi ba ya gane karatun boko. To ga abin da ya biyo baya:

Bayan Nura ya yi fice a garinsu a matsayin mahaddacin kur’ani kuma mutane suna yabonsa. Sai dai kash! Mahaifinsa da abokanan mahaifin suna masa kallon mutumin banza ne, saboda mahaifin nasa bai fada musu alherinsa, kullum sai dai ya fada musu cewa Nura dan iska ne wanda bai jin maganarsa. Wannan ya sa suka tsane shi, kuma suke zaginsa tare da fada wa mutanen da suke yabonsa cewa dan iska ne kawai. Haka labarin ya rika yawo a cikin mutanen garin, idan mutum ya ce bai yarda ba, sai a ce masa ai mahaifinsa ne na fada hakan, kuma ai babu wanda ya kai mahaifinsa kaunarsa.

Ita da mahaifiyarsa kullum tana cikin yi masa addu’a da kauna irin ta da da uwa. Kulluma addu’arta ita ce Allah Ya sa mahaifin ya gane ya fahimci cewa fa dole sai Allah Ya tambaye shi a kan kiwon da aka ba shi.

Shi dai mahaifin na Nura ya ja daga, bai ko sauraren mahaifiyar, ballantana sauran mutanen gari. Hasalima cewa yake yi ita ce take daura wa Nura gindi yake abin da ya gadama. Ita kuma a ganinta, ai Nura yana kan hanya madaidaiciya, don haka ya rage wa mahaifin hanya ce kawai ta sauke nauyin da Allah Ya dora masa. A ganinta ai ba dole bane ilimin boko, kuma ba dole bane sai an samu duniya. Tana cewa ai duk zafin neman ba ya kawo samu, amma kuma dole a kula da tarbiya domin shi ne abin tambaya a filin kiyama ba abin duniya ba. 

Daga baya Nura ya fara shiga cikin wani hali. Mutanen gari yawancinsu ba sa fadin alheri a game da shi duk da cewa a cikin zuciyarsa bai da komai sai alherin. Kasancewar Hausawa suna cewa “fata na gari lamiri” sai mugun fatan da mahaifin ke yi masa ya fara tasiri a kansa. Kawai sai aka wayi gari Nura na bin abokanan banza.

Ana cikin haka, sai watarana Nura ya samu mahaifinsa a zaune a cikin daki. Ya ce “baba me ya sa ba za ka mi fatan alheri ba. Mutane suna zagina a cikin gari, kuma kullum suna kafa hujja da cewa kai ne ka fada musu cewa ni mutumin banza ne. Don Allah ka yafe min idan ma na maka laifi ne, amma har ga Allah ba ni da laifi a wajen Allah.”

Bude bakin mahaifin ke da wuya sai ya hau fada yana cewa “ai ba karya bane, kai dan iska ne. Ka je can ka yi rayuwarka tun da ba za ki yi karatu ba, babu ruwana da kai.”

Nura ya tashi yana kuka yana mamakin wai mahaifnsa yana cewa ba ya son karatu, duk da cewa har musabaka ya ci na karatun kur’ani. Sai ya yi addu’ar Allah Ya sa mahaifinsa ya gane.

Kwatsam sai abokanan banza suka rinjayi Nura. Ya fara shaye-shaye, kamar wasa tun yana yi a boye, har ya kai ga cewa mutanen gari sun fara ganewa. Daganan sai mutanen gari suka fara cewa ai dama mahaifinsa ya fada cewa dan iska ne a boye gashi abin ya fito fili. Dagan an sai kowa ya fara Allah wadai da halinsa.

Mutane suna kara tofa albarkacin bakinsu, Nura na kara nisa a cikin aikin ashsha. Shi mahaifin ko a jikinsa, ita kuma mahaifiyar ta shiga cikin damuwa.

Nura ya yi nisa a cikin shaye-shaye, har ya fara kwace da sata a cikin garin da a da can aka san shi a matsayin malamin kur’ani. Haka zai sha miyakun kwayoyi yana tafiya yana maye, amma kuma yana raira karatun kur’ani.

Watarana suka je suka yi babban fashi har aka kama su aka kai su gidan kaso. Nura ya yi zaman gidan maza na wani dan lokaci. Da ya fito sai abin ya ci gaba. Tun abin bai damun mahaifin, har ya kai ga an fara zuwa gida ana kama shi.

Watara sai da ya yi kwana 15 a wajen ‘yan sanda a kan ko dai Nura ya zo ko kuma a ci gaba da rike shi. Nura ya aiko wa ‘yan sandan cewa idan dai mahaifinsa ne sai dai su kasha shi don ba zai zo ba. Sannan ya ce musu da mahaifiyarsa aka kama, da ko awa daya ba zai yi ba zai kawo kan shi domin yana son mahaifiyarsa kamar yadda take sonsa.

A haka dukiyar mahaifin ya kare wajen yawon zuwa wajen ‘yan Sanda. Watarana gidansa guda daya tak da yage, sai ga ‘yan sara suka sun fado gidan da niyyar daukar fansa, wai Nura ya sara wani daga cikinsu. Haka suka rusa gidan, sannan suka kora kowa da ke ciki. 

Wannan ne ya sa Nura ya bar garin ya koma Legas ya ci gaba da abin da ya gadama. Ita kuma mahaifiyarsa ta ci gaba da yi masa addu’a. Shi kuma mahaifin nasa ya shiga talauci da damuwa na yanayin da ya shiga.

Nura yana cikin wannan halin, sai addu’ar mahaifiyarsa ya isar masa. Sai ya ji cewa mahaifiyarsa tana fama da ciwo mai tsanani. Wannan ya sa Nura ya fara dawowa hayyacinsa. 

Kawai sai ya hadu da wani malami a can da yi sanadiyar nutsuwarsa sannan ya samu aiki yana yi a can Legas sannan ya ci gaba da karatunsa na kur’ani.

Daga baya ya zo gida ya biya kudin asibitin mahaifiyarsa, sannan ya koma Legas ya ci gaba da rayuwa. Domin a cewarsa ba zai iya ci gaba da zama a garinsu ba domin mutane suna masa kallon dan iska ne.

Sai ya koma Legas ya ci gaba da zama yana koyar da kur’ani kuma yana sana’a, sannan kuma yana taimakon iyayensa daga arzikin da Allah Ya bas hi.

Za a iya samun Isiyaku Muhammed a lambar waya: 07036223691