Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban labarin Hannatun Keffi da muka fara kawo muku a makon jiya. A makon jiya mun tsaya a wurin da Bashir da Ibrahim suke kallon Hannatu wanda hakan ya sanya ta tashi daga wurin da take zaune zuwa bangon dakin na barin gabas. Muna fata za ku ci gaba da bin labarin sau-da-kafa don jin yadda za ta kasance tsakanin Bashir da Hannatu da kuma Ibrahim.
Ni da Ibrahim muka ci gaba da kallonta a lokaci guda tausayinta ya yi uwa da-makarbiya a zuciyata. Na hada ido da Ibrahim, sannan na kalli gandiroban da yake kusa da shi. Abin da ya ba ni mamaki shi ne, shi ma gandiroban tausayi ne ya mamaye fuskarsa.
Bayan na kalli gandiroban ne ya kalle ni, sannan ya sake tafiyar da kallonsa ga budurwar da daga baya na san sunanta Hannatu (ba sunan gaskiya ba). Daga nan na matsa kusa da shi, sannan na fuskance shi, hakan ya sa ya mayar da hankalinsa gare ni. “Idan da hali zan so na gana da wannan budurwar don na san abin da ya dada ta da kasa, domin a zahirin gaskiya na damu kwarai don na ji labarin da ya yi sanadiyyar kawo ta gidan yari.” Na ce da gandiroban.
“Ba zan iya maka izini ba har sai na sanar da na gaba da ni, wanda shi ne zai yi maka izinin ganawa da ita.” Ya ce da ni kai-tsaye yana kallonsa. Na kalli Ibrahim, shi ma ya kalle ni. Daga baya ya ce bari ya karasa aikin da yake yi, tun da sauran kadan ya kammala, idan ya so sai mu nemi izini. Ban yi gardama ba bayan na kalle ta na ci gaba da bin su a baya. Har Ibrahim ya kammala uzurinsa ina tunanin ta.
Bayan mun kammala ne muka sake biyowa ta bangaren su Hannatu, har yanzu dai tana wurin da muka bar ta. Jin tafiyarmu ya sa ta dago kai, bayan mun hada ido ne na yi mata murmushi, nan-da-nan ta sunkuyar da kanta. Daga nan na san ta fara tunanin ni wane irin mutum ne. A dalilin kallonta da nake yi ne har na yi karo da Ibrahim. Ya juyo da sauri, sannan ya tambaye ni ko lafiya? Ban ce komai ba face nuna masa Hannatu da na yi, bayan ya kalle ta ne ya ci gaba da kallona yana tafiya, a lokaci guda yana jijjiga kai, haka muka ci gaba da tafiya har muka koma wurin karbar baki. Daga nan na nemi gandiroban ya hada ni da ogansa don in nema izinin ganawa da Hannatu. Bai yi musu ba, ya yi mana jagora har ofishin ogansu. Bayan ya yi mana iso ne, na gabatar masa da kaina hade da sanar da shi manufata na son jin labarin Hannatu. Na ce masa labarin zai zama izina ga jama’a. Ganin muhimmancin dalilina ne ya ce a yanzu lokaci ya kure sai dai na dawo gobe da misalin karfe 2:00 na rana. Na yi masa godiya tare da alkawarin zan dawo gobe in sha Allahu, sannan muka fita.
Gandiroban ya yi mana rakiya har zuwa wurin da muka yi wa motarmu matsugunni. A nan nake tambayarsa sunansa inda ya ce mini sunansa Hassan, shi da Ibrahim unguwarsu daya. Ibrahim shi ma ya tabbatar mini da hakan. A karshe muka yi sallama.
Tun da muka bar gidan yarin na rasa walwala, Ibrahim ya gane hakan amma sai ya kyale ni bai ce komai ba, ya san ni sarai ko yaya zai yi ba zan ce masa komai ba. Har ya ajiye ni a gida muka yi sallama duk da cewa ban ji labarinta ba, amma ina cikin juyayi. Ina tuna lokacin da zai ja motarsa ne ya zolaye ni, inda ya ce “an yi wa wani kamun kazar kuku.” Ban tanka masa ba saboda na gane inda ya dosa. Haka na shiga gida jikina babu kwari. Abin ya rika ba ni mamaki domin a daren ranar na kasa yin lafiyayyen barci sai sake-sake nake yi.
Za mu ci gaba a makon gobe in sha Allahu.