✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Giwa da Tela

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Giwa da Tela. Labarin na nuna bai kamata…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Giwa da Tela. Labarin na nuna bai kamata a rika amfani da bacin ran wani don hukunta wani ba.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi.

Labarin Giwa da Tela

An yi wata giwa a wani kauye, wadda ba ta tsokanar mutanen garin. Kullum idan ta fito daga gidanta za ta je kogi wanka, sai ta bi ta gaban shagon wani tela. Telan yakan kira ta ya ba ta abinci. Hakan ya sa suka shaku sosai suka zama abokai. Tsabagen yadda ta saba da telan idan ta zo wucewa, sai ta sanya bakinta a shagonsa, shi kuma sai ya ba ta abinci.
Rannan tela ya yi fada da masu kawo masa dinki. A takaice dai yana cikin bacin rai, sai giwa ta zo wucewa ta sanya bakinta a shagon tana tsammanin ta ji abinci a bakinta. Sai ta ji ya soka mata allura. Sai ta janye cikin sauri, sannan ta tafi abinta.
Daga nan ta wuce zuwa kogi, tana cikin wanka sai lakar cikin ruwan ta toshe mata hanci. Da ta zo komawa gida, sai ta tsaya a gaban tela a kan kayan dinkunnan da aka ba shi ta feso masa wannan tabon, ya bata masa kayansa.
Don haka nake janyo hankalin Manyan Gobe kada bacin rai ya sa su hukunta wanda bai yi musu laifi ba.